Header Ads

Sarkin Saudiyya ya gayyaci shugaban kasar Iran ya kawo ziyara Riyadh bayan cimma yarjejeniya a tsakanin su

Sarkin Salman

Sarkin Saudiyya, Salman bin Abdulaziz Al Saud, ya gayyaci shugaban kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ibrahim Raeisi, da ya kawo ziyara kasar, bayan cimma yarjejeniya a tsakanin kasashen nasu wadda kasar Sin ta jagoranta.  

Mohammad Jamshidi, wanda shine mataimakin shugaban kasar a bangaren harkokin siyasa, ne ya bayyana hakan a shafin sa na Twitter a ranar Lahadi, inda ya bayyana cewa sarkin ya aiko da wasika.

"A cikin wasika zuwa ga shugaban kasa Raeisi, sarkin Saudiyya ya yi maraba da yarjejeniyar da aka cimmawa a tsakanin kasashen 'yan uwan juna, ya kuma gayyace shi zuwa Riyadh." Kamar yadda ya bayyana, inda ya ce sarkin ya yi kira da a samar da hadin kai na yanki da tattalin arzuki a tsakanin kasashen biyu.

Babban jami'in na kasar Iran ya bayyana cewa shugaba Raeisi ya yi maraba da wannan gayyata.

Ana dai kallon wannan gayyata a matsayin wani babban mataki na kara karfin dangantaka a tsakanin kasashen biyu. 

Bayan kwanaki na sasantawa wanda kasar Sin ta jagoranta, kasar Iran da Saudi Arabiya sun cimma matsaya a ranar 10 ga watan Maci, inda za su cigaba da huldar diflomasiyya tare da bude ofishin jakadanci da na wakilansu a kasashen a cikin watanni biyu.

Kamar yadda wani jawabi na hadaka wanda suka yi ya nuna, kasashen sun yarda da muhimmancin girmama iyakokin juna da kuma rashin yin shishshigi cikin al'amurran cikin gida na juna.

Sun amince su tabbatar da wata yarjejeniya ta tsaro wadda aka sanyawa hannu a cikin watan Afirilun shekarar 2001 da kuma wata yarjejeniya wadda aka cimmawa a watan Mayun 1998 ta habaka hadin kai ta fuskar tattalin arzuki, kasuwanci, sa jari, kere-kere, kimiyya, al'adu, wasanni da harkokin da suka shafi matasa. 

Kasar Saudi Arabiya dai ta yanke huldar diflomasiyya da Iran ne a shekarar 2016, bayan da 'yan kasar Iran masu zanga-zanga sakamakon fusata da suka yi kan kisan babban malami Sheikh Nimr Baqir al-Nimr da Saudi Arabiya ta yi, suka afka ofishin jakadancin Saudiyyar da ke Tehran.

Bangarorin biyu sun yi zaman sasantawa har sau biyar a babban birnin kasar Iraki, Bagadaza, tun bayan watan Afirilun shekarar 2021.

No comments

Powered by Blogger.