Sama da mutane 10,000 suka muta a Amurka a shekarar nan sakamakon harbe-harben bindiga
Sama da mutane 10,000 suka mutu a Amurka a cikin wannan shekarar sakamakon harbe-harben bindiga, wanda ke nufin akalla mutane 111 kenan a rana, kamar yadda binciken wata kungiya mai zaman kan ta ya nuna.
Rahoton baya-bayan nan daga Gun Violence Achieve ya nuna cewa mutane 5,742 sun kashe kan su da bindiga a yayin da kuma wasu 4,266 suka mutu ta hanyar aikata kisan kai, wasu su kashe su, yayin kariyar kai da sauransu.
A cikin kananan yara, yara 59 wadanda shekarunsu suka kama zuwa 11 suka mutu a cikin irin wannan yanayi da kuma wasu 347 masu shekaru 12 zuwa 17, kamar yadda binciken ya nuna.
Rahoton ya nuna cewa akwai harbe-harbe da aka yi na kan-mai-uwa-da-wabi har 130 a wannan shekarar kawai, kuma harbe-harben na karuwa a cikin shekarun nan.
A cikin shekaru uku da suka gabata, akwai harbe-harben kan-mai-uwa-da-wabi sama da 600 a cikin shekarun, kusan sau biyu a kowacce rana.
An dai saki rahoton ne bayan harbe-harben da aka yi a jihar Tennessee da ke Amurka a ranar Litinin, inda yara uku da kuma wasu manyan mutane uku suka rasa rayukansu a wata makarantar elementary ta kiristoci wadda ba ta gwamnati ba.
Wanda ya kai harin, wanda tsohon dalubin makarantar ne, shima ya rasa ransa yayin harbe-harbe da wasu 'yan sanda mutum biyar.
Wannan harbe-harbe na zuwa ne a yayin da al'ummu a Amurka ke fama da yawan harbe-harben bindigogi, ciki har da kisan kiyashin shekarar da ta gabata a jihar Texas a wata makarantar elementary inda dalubai sha tara da malamai biyu suka rasu.
Shugaban kasar Amurka, Joe Biden, a ranar Talata ya yi kira ga majalisar Congress da su zartar da doka wadda za ta kawo karshen matsalar bindigogi a kasar.
A ranar Litinin, ya yi kira ga majalisar Congress ta Amurka da ta sake dawo da dokar da ta haramta amfani da makaman da za a iya kai hari da su, wadda ta ke a tsakanin shekarar 1994 zuwa 2004.
Wannan kira na Biden ya gamu da rashin amincewa daga 'yan majalisar Amurka na karkashin jam'iyyar Republican, wadanda sune manyan magoya bayan 'yancin mallakar bindiga.
Wani binciken jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a Amurka a cikin watan Oktobar shekarar 2022 ya nuna cewa mafi yawan mutanen Amurka suna goyon bayan daukar mataki a kan bindigogi, inda kashi 57 cikin 100 na 'yan Amerikan suka nuna cewa suna bukatar a yi dokoki masu tsauri kan sayar da bindigogin.
Post a Comment