Header Ads

Sabon Sarkin Dutse Hameem Nuhu ya karbi sandar sarauta


Sabon sarkin Dutse, Alhaji Hameem Nuhu Muhammad Sunusi, na karbar sandar mulki daga gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Abubakar Badaru.

An gudanar da kasaitaccen biki a ranar Asabar a filin taro na Aminu Kano da ke Dutse, jihar Jigawa, domin nadin sarautar sabon sarkin Dutse, Alhaji Hameem Nuhu Sunusi.

Wannan biki dai ya samu halartar dubban mutane a ciki da wajen jihar Jigawa domin taya sabon sarkin murnar yin nadin nasa.

A yayin nadin sarautar, gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Abubakar Badaru, ya mika sandar mulki ga sabon sarkin na Dutse, Alhaji Hameem Nuhu Muhammad Sunusi, inda ya ce yana fata sabon sarkin ya dora kan irin abubuwan bajintar da mahaifinsa, marigayi Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi, ya yi.

Cikin mahalarta bikin nadin sarautar, bayan gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Abubakar Badaru, akwai tsohon gwamnan jihar Borno kuma zababben mataimakin shugaban kasa, Kashin Shettima, sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, sarkin Borno, Abubakar Ibn Umar El-Kanemi, sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar da kuma sarkin Sokoto, Alhaji Sa'ad Abubakar III.

No comments

Powered by Blogger.