Muzaharar lumana: Tawagar Elrufai ta kashe mutum 5 a Kaduna
Da misalin karfe 3:00ny ne a yau Alhamis 16/3/2023 'yan'uwa musulmi almajiran Sheikh Zakzaky na Kaduna suka fito muzaharar kira ga Gwamnatin Najeriya ta sakar ma Sheikh Zakzaky fasfo dinsa domin ya je neman lafiya, sai tawagar Gwamnan jihar, Elrufai, ta cim masu, ta bude musu wuta, tare da kashe mutum biyar.
Muzaharar, wadda aka fara daga Gwamna Road da ke kan shataletalen Bye Pass Kaduna na tafiya cikin tsari kamar yadda suka saba fitowa, 'yan'uwa maza da mata suna tafiya cikin tsari, sai ga Gwamnan jihar Kaduna, Elrufai, tare da rakiyan jami'an tsaro a cikin mota.
Zuwansu ke da wiya suka sauka suka fara harbin 'yan'uwa masu muzaharar a saki fasfo din Sheikh Zakzaky.
Ya zuwa lokacin rubuta rahoton nan jami'an tsaron Elrufai sun harbe mutum biyar tare da raunata mutane da dama.
Zuwa yanzu akwai tabbacin mutum biyar wadanda suka yi shahada.
Post a Comment