Mutane biyu sun rasu, da yawa sun jikkata a hatsarin jirgin kasa da motar bas a Legas
Hukumar kula da hanya ta jihar Legas ta bayyana cewa mutane biyu da hatsarin jirgin kasa na BTR ya shafa da safiyar Alhamis din nan sun rasu.
Daraktan hulda da jama'a da wayar da kan mutane a hukumar kula da hanyoyi ta jihar, Adebayo Taofiq, ya bayyanawa jaridar The Punch cewa motar na cike da ma'aikatan gwamnatin jiha ne, kuma direban ya kasa yin hakuri.
"Mutum ba zai iya lissafa ko mutane nawa ba ne a cikin motar bas din nan-da-nan haka shi ma jirgin kasan na BTR, wasu a tsaye suke domin bas din a cike ta ke. Direban ya kamata a ce ya tsaya jirgin kasa din ya wuce, domin ko karfe 8 na safe ba ta yi ba, menene na gaggawa?"
"Mutane biyu sun mutu a yayin da kuma jirgin kasa din ya tura motar zuwa waje mai dan nisa, yayin da wasu sun iya yin tsale daga motar wasu kuma sun kasa fita. An ceto mutane 15 yanzu haka, baza mu iya cewa ga adadin ba, amma mutum biyu sun mutu."
Taofiq dai ya tabbatar da afkuwar al'amarin tun a farko, inda ya bayyana cewa, "Wata motar bas mallakar gwamnatin jihar Legas, mai lamba 04A - 48LA a safiyar ranar Alhamis ta ci karo da wani jirgin kasa mai gudu a PWD, yankin Ikeja a Legas.
"Mutane da yawa sun samu raunuka a wannan hadari domin motar gwamnatin a cike ta ke da ma'aikata wadanda za su tafi aiki a wannan safiyar."
Post a Comment