Header Ads

MURIC ta gargadi matar gwamnan jihar Bauchi

An zargi matar gwamnan jihar Bauchi, Dakta Aisha Bala Muhammad, da yin barazana ga shugabannin kungiyoyin mata musulmai da suka ziyarci matar dan takarar gwamna a jihar ta Bauchi karkashin jam'iyyar adawa. 

Daraktan kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ne ya yi wannan zargi a ranar Asabar 25 ga watan Maris na shekarar 2023.

Farfesan ya gargadi Aisha da ta guji kara yin wani abu a gaba wanda ba daidai ba ga matan. 

"Ana ikirarin cewa matar gwamnan jihar Bauchi, Dakta Aisha Bala Muhammed, na shirin yin barazana ga shugabannin kungiyoyin mata musulmai wadanda suka kai ziyara ga matar dan takarar gwamna a jihar karkashin jam'iyyar adawa, Hajiya Sadiya, wadda ita ce ministar ayyukan jin kai.

"Hajiya Sadiya ita ce matar Air Marshal Abubakar Sadique, dan takarar kujerar gwamna a zaben da ya gabata na shekarar 2023 a karkashin jam'iyyar adawa wanda ya yi takara da gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed.

"Matan da a dukkan alamu kan iya fuskantar musgunawar siyasa sun hada da Amirah (shugaba) ta kungiyar mata musulmai ta FOMWAN, Amirah ta kungiyar mata musulmai ta IMWON da Amirah ta kungiyar mata musulmai ta Nisau Sunnah (Women of the Tradition).

" A yanzu haka, matar gwamnan ta bayar da umarni a kawo fayel din shugabar kungiyar mata ta Nisau Sunnah daga ofishin shugabar matar da ke Kwalejin Ilimi, Kangare. Ana kyautata zaton wasu matakan za su biyo baya ga sauran shugabannin kungiyoyin mata musulman guda biyu.

"MURIC ba ta amince da duk wani yunkuri na yin horo ba ga mata musulmai wadanda suke aiki domin addinin musulunci. Wannan cutarwa ne domin banbancin ra'ayi, musgunawa, tursasawa da yin amfani da karfi. Ikirarin kawo fayel din shugabar kungiyar musulmai mata ta Nisau Sunnah an yi shi ne saboda siyasa.

"Za mu tunkari wannan rashin adalcin da duk wani mataki da ya kamata mu dauka na ka'ida. Domin haka muna kira ga shugaban kungiyar MURIC, mambobin kwamitin zartarwar kungiyar da duka mambobin kungiyar da ke Bauchi su kasance a shirye domin jin umarni daga babbar cibiyar kungiya.

"Muna kira ga duka mambobin kungiyoyin FOMWAN, IMWAN da Nisau Sunnah da su kasance cikin shiri kuma su bar kofar sadarwa a tsakaninmu a bude. Babu wata mace mai yin fafutika domin musulunci da za ta sha wahala a banza. Saboda haka muna kira ga matar gwamanan jihar Bauchi da ta kauracewa wannan tunanin in ma har da gaske ne. Ka da ta kirkiro abinda ba ta san abubuwan da zai iya haifarwa ba."

No comments

Powered by Blogger.