Header Ads

Muhammad Umar Bago ya lashe zaben gwamna a jihar Neja

Muhammad Umar Bago na APC ya lashe zaben gwamnan Neja

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta bayyana dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar APC, Mohammed Umar Bago, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Neja.

Bago ya yi nasara ne da kuri'u 469,896 inda babban abokin takararsa, Alhaji Liman Isah Kantigi, ya samu kuri'u 387,476, sai kuma dan takarar gwamna a jam'iyyar LP a jihar, Joshua Bawa, wanda ya samu kuri'u 3,415.

Farfesa Clement Allawa, wanda shine jami'in tattara sakamakon zaben gwamna a jihar, ya bayyana haka a ofishin hukumar da ke Minna.

Farfesan ya bayyana cewa mutanen da suka yi rijistar zabe a jihar sune 2,698,344 a yayin da kuma wadanda aka tantance sune 899,488.

Farfesan ya kara da cewa kuri'un da aka kada da kyau sune 873,020 wadanda kuma ba a kada su da kyau ba sune 26,936, kuri'un da aka kada duka kuma sune 889,956.

Duka wakilan jam'iyyun da ke nan sun sa hannu a wannan sakamako, wakilin jam'iyyar PDP, Alhaji Sani Idris Kutigi, ne kawai ya ki sa hannunsa.

Wakilin bai bayyana dalilinsa na yin haka ba, to amma alama ce da ke nuna cewa basu amince da sakamakon ba kuma tana iya yiwuwa su tafi kotu domin kalubalantar sakamakon.

No comments

Powered by Blogger.