Menene dalilin 'yan sanda na kama shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai?
'Yan sanda sun kama shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai ta kasa, Hon. Alhassan Ado Doguwa, bisa zargin sa da hannu cikin kisan mutane da dama da kuma kona ofishin jam'iyyar NNPP a yayin zaben shugaban kasa da aka kammala.
Alhassan Ado-Doguwa, wanda ke wakiltar mazabar Tudun Wada da Doguwa, dan jam'iyya mai mulki ne ta APC, kuma hukumomin 'yan sanda sun tabbatar da kama shi a filin jirgin saman kasa-da-kasa na Aminu Kano da ke Kano.
An ma yi zargin cewa ya yi amfani da karamar bindiga inda ya harbi mutane da ita.
Dan majalisar wanda aka yi ikirarin ya jagoranci batagari wajen kona ofishin jam'iyyar ta NNPP, inda kuma mutane uku suka rasu, an bayyana cewa yanzu haka yana ofishin binciken manyan laifuka.
Yayin da suke tabbatar da afkuwar al'amarin, rundunar 'yan sandan jihar ta Kano ta bayyana cewa akalla mutane uku ne suka rasu yayin da aka sa wuta a ofishin jam'iyyar ta NNPP, inda kuma mutane biyu suka rasa ransu ta hanyar konewa yayin da ake tattara sakamakon zaben 'yan majalisu wanda kuma aka bayyana cewa Alhassan Ado Doguwa din ne ya yi nasara.
Kafin dai kamen nasa, a yayin da yake tattaunawa da manema labaru, Doguwa ya musanta hannun sa a cikin al'amarin tare da bayyana cewa har yanzu 'yan sanda basu gayyace shi ba, inda ya ce, "Ni ban ruke bindiga ba, ban ma san yadda zan ruke bindiga ba. Gabadaya a yayin zaben ban ruke makami ba."
Post a Comment