Menene dalilin tashin gobara a sansanin 'yan gudun hijiran Rohingya?
Wata babbar gobara a ranar Lahadi ta tashi a sansanin 'yan gudun hijirar Rohingya da ke kasar Bangladesh, dalilin haka kuwa sama da tantuna 2,000 ne suka kone kuma mutane sama da 12,000 suka rasa wurin kwanansu kamar yadda Mijanur Rahman, kwamishinan 'yan gudun jihira a Bangladesh, ya bayyana kididdigar.
Sansanin wanda ke kudu maso gabashin kasar Bangladesh, shine sansanin 'yan gudun hijira mafi girmaa duniya kuma mafi yawa musulman Rohingya ne su miliyan daya a cikinsa wadanda suka baro Myanmar saboda gallaza masu.
An samu sa'ar kashe gobarar cikin sa'o'i uku, kuma a ranar Litinin mutane suka koma sansanin domin ganin irin barnar da gobarar ta yi, bayan kona tantunan ta ma kona masallatai 35 da dakunan karatu 21.
Sansanin shine matsugunnin 'yan gudun hijira musulmin Rohingya wadanda hukumomin Myanmar ke gallaza mawa.
Kasar ta Myanmar na dauke da miliyoyin mabiya addinin Budda kuma 'yan Rohingya, wadanda tun a shekarar 2017 suke zaune a kasar Bangladesh a matsayin 'yan gudun hijira, ba su da yawa.
Tuni dai hukumomi a Bangladesh suka dukufa wajen bincike domin gano dalilin afkuwar wannan gobara a sansanin.
Post a Comment