Header Ads

Me ya sa aka mai da shari'ar Hadiza Gabon zuwa babbar kotun Shari'a?


Jarumar fim, Hadiza Aliyu-Gabon

Wata kotun shari'a da ke Magajin Gari a Kaduna ta mayar da karar da aka shigar kan jarumar fim, Hadiza Aliyu-Gabon, ta zargin yin cuta da yaudara zuwa Babbar Kotun Shari'a.

Alkalin kotun, Malam Isiyaku Abdulrahman, ya mayar da karar zuwa babbar kotun ne bayan rokon da mai ba wanda ya shigar da karar shawara ta doka, Malam Nurudeen Murtala, ya yi.

A yayin da ya ke mayar da gudanar da shari'ar can, Alkalin ya zargi mai bayar da shawarar ta doka ga wanda ya shigar da karar da kokarin batawa kotu lokaci.

"Kuna da zabi guda biyu, ko dai in kori shari'ar nan ko kuma a mayar da ita wata kotun." Alkalin ya bayyana.

Bala Musa, wani ma'aikacin gwamnati, ya kai karar jarumar fim din ne sakamakon kin aurensa da ta yi. 

Kamar yadda Musa ya shaidawa kotu, "Zuwa yanzu na kashe kudi sun kai 396,000 a kan ta. Duk lokacin da ta bukaci kudi ina ba ta ba bata lokaci da fatan za ta aure ni."

Wadda ake karar, ta bakin mai ba ta shawara ta doka, Barista Mubarak Sani, ta musanta sanin Musa ko ma ganin shi da kuma wata mu'amala a tsakaninsu ta kowacce fuska.

Mai bada shawarar shari'a ga wanda ya shigar da karar ya samar da kwafin bayanan banki inda ya bayyana cewa wasu mutane hudu su ke karbar kudaden inda suka tabbatar da cewa wadda ake kara suke ba kudaden.

Biyu daga cikin mutanen, Fatima Abdullahi da Yusuf Abdullahi, sun yin ikirarin cewa su bokai ne kuma mataimakan wadda ake kara.

Sun dai amsa laifinsu na yin abubuwa da kuma karbar kudade da sunan jarumar, inda suka roki kotu da ta yafe masu.

No comments

Powered by Blogger.