Masu zanga-zanga a Isra'ila sun sha alwashin cigaba
Wata shugabar masu zanga-zanga a Isra'ila ta sha alwashin cigaba da gudanar da zanga-zanga a yankunan da Isra'ila ta mamaye a yayin da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya sanar da cewa za a dakatar da yin canje-canje ga sashen shari'ar kasar har sai wata mai zuwa.
"In har wadannan canje-canje sun cigaba da kasancewa ba wai dakatar da su aka yi ba, za mu kasance kan tituna." Shikma Bessler, wata shugabar masu zanga-zanga ta bayyana bayan Netanyahu ya gabatar da jawabi ta talabijin a ranar Litinin.
Bessler ta bayyana cewa Netanyahu da shi da ire-irensa a fili ya ke suna so ne su cigaba da dokokinsu na mulkin mallaka a cikin majalisar Knesset mai zuwa wadda za ta fara aiki nan da wata daya.
Ta bayyana cewa canje-canjen, wadanda za su rage karfin kotu a kan sashen majalisar dokoki da sashen zartarwa, tare da ba majalisar Knesset ikon yin watsi da umarnin kotu da kuri'u 61 a cikin 120, na da cutarwa ga "Tattalin arzuki da tsaron Isra'ila."
Netanyahu ya bayyana a ranar Litinin cewa zai dakatar da kudurin yin canje-canje ga sashen shari'ar na dan wani lokaci. Amma ya bayyana cewa yana nan kan kudurinsa na yin canje-canjen.
Wannan dai hatsaniya ta kulle mafi yawan biranen kasar kuma tana yin barazana ga tattalin arzuki, tsayar da tashar jiragen sama a babban filin jiragen sama na kasa-da-kasa na Ben Gurion sannan kuma ayyuka sun tsaya a tasoshin jiragen ruwa.
An kulle makarantun yara, shaguna da reshen shagunan sayar da abinci wanda aka sarrafa.
Wannan fafutika a kan shirin canje-canjen na yin nuni ne da irin darewar da ke tsakanin al'ummar Isra'ila tsakanin masu goyon bayan gwamnati, wadanda suka ce canje-canjen na da muhimmanci, da kuma mutanen da suka fi yawa wadanda basu goyon bayan shirin na Netanyahu, wadanda suka ce wannan al'amari zai rage karfin bangaren shari'a ne.
Post a Comment