Manzon Allah Ya Ce Ba A Cizon Mumini Sau Biyu A Rami Daya In ji Hon. Sani Sha'aban
Daga Nasiru Adamu
A wata tattaunawa da dan takaran Gwamnan jihar Kaduna karkashin jam'iyar ADP Hon. Muhammad Sani Sha'aban Dan Biron Zazzau ya yi da Radiyon tarayya na Kaduna, a karshen makon da ya gabata, ya bayyana cewa zai zama babban sakarci ne da rashin tunani maimaita kuskure sau biyu a lokaci guda ga Mumini mai tsoron Allah, ballantana har ya aikata a karo na uku. Domin kuwa Manzon Allah ya ce ba a cizon mumini sau biyu a rami daya.
Hon. Sha'aban Danburan Zazzau, ya ce batun da wasu jam'iyyu ke kira ga a yi "Muslim-Muslim Ticket" kuwa yaudara ce da mai da mutane gidadawa, domin kuwa har ya zuwa yau ba abin da al'ummar kasar nan, musamman ta jihar Kaduna ke fama da shi, in banda wahalhalu tare da barazanar kuntatawa jama'a. Wanda su da kansu suka fada cewar za su dora daga inda tsohuwar gwamnatin su ta bari. Me wannan ke nufi ?
Haka nan Hon. Danburan Zazzau ya yi takaicin yadda wasu malaman addinin Musulunci ke hawa kan Mimbarin sallar Juma'a ko Masallatan Unguwanni suna goyon bayan irin wadannan miyagun shuwagabannin har suke gaskata abin da suke fada saboda dan abin da aka ba su.
Haka nan ya ce, an kammala shekaru 16 a can baya, sannan aka sake maimaita shekaru 8 ana cutar da mutane, yanzu ana bin su da dadin baki tare da taliya bibbiyu don a gallaza masu na wasu shekaru 4 ko fiye da haka a nan gaba. "Ya kamata talaka ya fadaka kuma ya gane yana da bukatar canji," in ji shi.
Da aka tambayi ra'ayinsa a kan matsayinsa a kan walwalan mutane a matsayinsa na dan takaran neman kujerar gwamnan jihar Kaduna a karkashin tutar jam'iyyar ADP, idan Allah ya sa hakarsa ta cimma ruwa? Sai ya ce, a matsayin sa na musulmi wanda ya taso gidan mutunci da sanin mutuncin danAdam zai mutumta dukkanin Kabilu da Addinan Musulunci da Kiristanci tare da al'adun su, domin zai zama tozarta addinin Musulunci a gare shi matukar ya yi sabanin abin da addininsa ya koyar da shi. Domin samun daukaka ta hanyar addini shi ya fi duniya da lahira ga mutum.
Post a Comment