Majalisar kasar Afirka ta Kudu ta amince da rage karfin dangantakar kasar da Isra'ila domin nuna goyon baya ga Falasdinawa
Majalisar kasar Afirka ta Kudu ta amince da rage karfin dangantakar da ke tsakanin kasar da kasar Isra'ila domin nuna goyon baya ga Falasdinawa.
Majalisar ta amince da babban kudurin ne a ranar Talata kamar yadda kafar watsa labaru wadda ke Ingila ta Middle East Eye ta bayyana a shafinta na labarai da sharhi.
Kudurin yin hakan dai wata jam'iyya ce mai suna National Freedom Party (NFP) ta shigar da shi tana neman a rage darajar ofishin jakadancin kasar da ke yankunan da aka mamaye sakamakon cigaba da tursasawar da Isra'ila ke yiwa Falasdinawa.
Jam'iyyar ta NFP ta bayyana cewa irin wannan yunkuri tabbas zai samu goyon baya daga shugaban kasar marigayi Nelson Mandela wanda ya ke yaki da wariyar launin fata.
"Wannan wani lokaci ne wanda Nelson Mandela zai yi alfahari da shi. A kodayaushe yana fadin cewa 'yancin mu ba zai cika ba har sai Falasdinawa sun samu 'yancin su."
An gina Isra'ila ne "Ta hanyar kora, kisan kai da cutarwa ga Falasdinawa. Domin su iya yin mulki, sai suka kafa wariyar launin fata domin su iya mulkar Falasdinawa." Kamar yadda ya ke a cikin jawabin
"A matsayinmu na 'yan Afirka ta Kudu ba za mu zura ido muna kallo ana sake maimaita wariyar launin fata ba."
Isra'ila ta ginu ne a shekarar 1948 bayan ta mamaye kasa mai fadin gaske ta Falasdinawa a yayin wani yaki wanda yammacin duniya ya goyi baya.
Ta kara mamaye wurare da dama wadanda suka hada da yamma da gabar kogin Jordan, gabashin al-Quds da zirin Gaza, a wani yakin kuma a shekarar 1967. Isara'ila ta janye daga Gaza a shekarar 2015, amma ta kasance ta kan yi hare-hare ga wurin tare da killacewa mara kyau ga yankin.
Post a Comment