Majalisar dinkin duniya ta yi Allah wadai da kisan da aka yi wa fararen hula a jihar Borno
Majalisar dinkin duniya ta yi Allah wadai da kashe fararen hula sama da 30 wanda ake zargin mambobin kungiyar ISWAP ne suka yi a karamar hukumar Gamboru Ngala ta jihar Borno.
Fararen hular dai mafi yawansu masu kamun kifi ne, kuma wasu fararen hula da abin ya shafa tuni aka tafi da su asibiti domin kulawa da lafiyarsu.
Mai kula da ayyukan agaji na majalisar dinkin duniya a Nijeriya, Matthias Schmale, ne ya yi Allah wadai da kisan a cikin wani jawabi da ya fitar da yammacin ranar Alhamis a Abuja.
Schmale ya bayyana damuwarsa a kan al'amarin wanda ya faru a kauyen Mukdolo da ke kan bakin boda, inda ya bayyana cewa bayan wannan mummunan hari da aka kai, fararen hula da dama sun bace ba a gan su ba.
"Wadanda wannan mummunan hari ya shafa fararen hula ne masu kamun kifi da manoma wadanda ke neman halaliyarsu a wannan muhalli da ba ya da tsaro. Sun hada da 'yan gudun hijira da kuma mutanen wajen na asali da suka karbe su daga karamar hukumar Dikwa.
"Wannan harin abin mamaki ne kuma wata mummunar tunatarwa ce ga irin barazana ta hadari da rashin tsaro irin wanda 'yan gudun hijira da sauran mutane ke fuskanta a tsawon shekaru 13 na tashin hankali wanda ba yaki ne na kasa-da-kasa ba wanda yankin ke fuskanta a kullum a kokarin mutanen wajen na su samu su tsira.
"Kafin harin, mutane sun kauracewa kauyen Mukdolo sakamakon fadace-fadace na kungiyoyi masu dauke da makamai.
"Ina kira ga duk wadanda za su iya yin wani abu dangane da wadannan rikice-rikice da su sauke nauyin da ke kansu a karkashin dokokin jin kai da hakkokin bil-adama na kasa-da-kasa domin kare fararen hula daga cutuwa.
"Ina kuma kira ga hukumomi da su gaggauta yin bincike cikin wannan laifi kuma su gaggauta kamo wadanda suka aikata wannan al'amari domin su fuskanci hukunci." Kamar yadda Schmale ya bayyana.
Jihar Borno ta kasance wata cibiya ta masu tada kayar baya na 'yan Boko Haram a tsawon shekaru 13, sakamakon haka mutane da yawan gaske sun rasa rayukansu kuma miliyoyi sun bar muhallansu tun shekarar 2010. Ita ma kungiyar ISWAP ta shiga cikin jerin baraza ga yankin, inda ta ke fada da kungiyar Boko Haram domin samun iko.
Post a Comment