Header Ads

Majalisar dinkin duniya ta gabatar da ranar yaki da "Islamophobia" ta duniya irin ta na farko

Hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya (UN) da ke New York, Amurka

Majalisar dinkin duniya ta gabatar da ranar kalubalantar abinda ake kira "Islamophobia" na duniya, irinta na farko wanda ya gudanar a zauren majalisar da ke birnin New York a ranar Juma'a.

Kamar yadda littafin Kamus na yanar gizo na Wikipedia ya yi bayanin kalmar, ya ce, "Islamophobia shine tsoro, kiyayya, ko nuna wariya ga addinin musulunci da musulmai gaba daya, musamman in ana ganinsu na wani yanki ne ko kuma tushen ta'addanci." 

Wakilin Hukumar dillancin labaru ta Nijeriya (NAN) a majalisar dinkin duniya, ya yi rahoton cewa masu gabatar da kasidu a yayin taron sun nuna cewa akwai bukatar daukar babban mataki in an yi la'akari da kara hauhawar nuna banbanci ga musulmai da tursasawa a garesu.

An tabbatar da ranar ne ta zama ta duniya biyo bayan wani kuduri da aka shigar cikin watan Maris din shekarar 2022 wanda ya yi kira da a tabbatar da zama da juna cikin mutunci duk da banbanci da ke tsakani, zaman lafiya, girmama hakkokin bil-adama da kuma addini.

Kamar yadda sakataren majalisar dinkin duniya, Antonio Gutterres, ya bayyana, ya ce musulmai wadanda sun kusa kaiwa biliyan 2 a duniya kuma wadanda sun fito ne daga kowanne bangare na duniya, "suna wakiltar bil-adama ne na kowanne bangare" to amma wani lokacin sukan fuskanci musgunawa kawai saboda imaninsu.

Bayan haka "mata musulmai na iya fuskantar musgunawa wadda ta lunka sau uku saboda jinsin su, yarensu da imaninsu."

Babban taron dai ministan kasashen waje na Pakistan, Mista Bilawal Zardari, ne ya shugabance shi, inda ya bayyana cewa musulunci addini ne na zaman lafiya da zama da sauran mutane cikin mutunci.

Duk da cewa Islamophobia ba abu ne sabo ba, amma "abun bakin ciki ne a wannan lokaci namu" da karuwa kawai ya ke yi yana yaduwa.

"Tun bayan ibtila'in 9/11, kiyayya da zargi suka karu a kan musulmai da musulunci kamar annoba.

"An yi bayanai wadanda ke danganta al'ummomin musulmai da addininsu da hatsari da kuma tayar da hankali." Zardari ya bayyana, wanda kuma shine shugaban majalisar ministocin kasashen waje na kungiyar kasashen musulmai (OIC). 

Zardari ya bayyana cewa wannan abu da ake kira Islamophobia ba wai kawai kan masu tsatstsauran ra'ayi ya tsaya ba ko kuma farfaganda, sai dai abin takaici har ya shiga cikin kafofin watsa labaru, sashen ilimi, masu aiwatar da tsare-tsare da gwamnatoci.

Shugaban babban taron majalisar dinkin duniya, Mista Csaba Korosi, a nashi bangaren, ya bayyana ce Islamophobia na da tushe a cikin abinda ake kira Xenophobia, wato tsoron baki, wanda ke fitowa fili ta hanyar nuna wariya kala-kala, hana yin tafiye-tafiye da yin kalaman batanci da kuma kai ma wasu mutane farmaki.

Sai ya yi kira ga kasashen duniya da su tabbatar da hakkin addini da imanin da mutum ke da shi, wanda aka tabbatar da shi a karkashin abinda aka kira International Covenant on Civil and Political Rights.

No comments

Powered by Blogger.