Kwamishinan harkokin addini na jihar Sokoto ya rasu
Kwamishinan harkokin addini a jihar Sokoto, Alhaji Usman Suleiman, ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya a Sokoto.
Marigayin, wanda shine mai ruke da sarautar Danmadamin Isa, ya rasu ne a ranar Juma'a kuma tuni aka yi zana'idarsa.
Mutane da yawa sun samu halartar zana'idar marigayin, cikinsu akwai mataimakin gwamnan jihar ta Sokoto, Alhaji Mannir Dan'iya, Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Mainasara Ahmad, Shugaban Ma'aikata, Abubakar Dan-Shehu, shugaban jam'iyyar PDP a jihar, Alhaji Garba Goronyo da sauransu.
A cikin sakonsa na gaisuwa, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya bayyana marigayin a matsayin musulmi na kwarai kuma kwamishina mai aiki tukuru a duka ma'aikatun da ya ruke.
"A maimakon gwamnatin jihar Sokoto da mutanen jihar Sokoto, ina mika sakon ta'aziyya ta ga iyalansa." Kamar yadda Tambuwal ya bayyana.
Gwamnan ya yi addu'ar samun rahamar Allah ga ruhin mamacin da kuma kasancewar Aljannah ta zama makomarsa a lahira.
Post a Comment