Header Ads

Kungiyar Hamas ta harzuka da kisan da Isra'ila ke yi


Wasu sojojin Isra'ila

Kungiyar fafutika ta Falasdinawa, Hamas, ta harzuka sakamakon wani kudurin doka na zartar da hukuncin kisa wanda kasar Isra'ila ta aminta da shi, wanda kuma in ya zama doka, to zai halasta kashe Falasdinawan da suke a tsare wadanda suka nuna turjiya daga mamaya.

Kungiyar fafutikar ta bayyana fusata da ta yi ne a ranar Laraba, bayan da majalisar Isra'ila, Knesset, ta amince da kudurin, wanda ministan Isra'ila Itamar Ben-Gvir ya kirkiro , a karanta shi a majalisar.

Kungiyar ta yi Allah wadai da kudurin wanda ke son mayar da kashe-kashen Falasdinawa su kasance a kan doka ne, kamar yadda kafar watsa labaru ta Palestinian Information Center ta ruwaito a cikin wani jawabi na Hamas.

"Irin wannan nuna wariyar launin fatar da ayyukan laifukan na yin nuni ne da irin mulkin kama karya na Isra'ila.

"Wannan na nuna irin yadda kashe-kashen da sojojin Isra'ila ke yi hankali kwance ya kai matuka duniya kuma na kallo." Kamar yadda ya ke a cikin jawabin, inda suka sake tunatar da cewa dokokin kasa-da-kasa sun haramta kisa sakamakon wariyar launin fata da kuma hana hakki wanda mutum ke da shi.

Kungiyar ta Hamas ta tabbatar da cewa irin wadannan tsare-tsare ba za su taba hana Falasdinawa yin gwagwarmayar samun 'yancinsu ba a kan gwamnatin mamayar da kuma kawayenta.

Ko a ranar Laraba, sojojin Isra'ila sun kai hari wani sansanin 'yan gudun hijira mai suna Aqabat Jabr, inda suka yi mummunan rauni ga wani mutum da suke zargi ya kashe wani dan Isra'ila mai mota.

 Mahmood Jamal Hassan Hamdan, ya rasu sakamakon raunuka da harsasan sojojin mamayar suka harba masa.

Bayan rasuwar ta Hamdan dan shekaru 22, yawan Falasdinawan da Isra'ila ta kashe da kuma wadanda mazauna a Isra'ila suka kashe ya kai 67 a wannan shekarar kawai, hudu daga ciki harbin bindiga ne daga mazauna yankunan mamayar suka kashe su, yara 13, tsofaffi guda hudu da kuma wani da ya ke kurkuku mutum daya.

No comments

Powered by Blogger.