Kungiyar FOMWAN ta nemi a ba mata kashi 50% na guraben mukamai a gwamnatin Tinubu
Kungiyar mata musulmai ta Nijeriya, FOMWAN, ta nemi gwamnatin Tinubu da ta ba mata kashi 50 cikin dari na matsayi saboda gudummuwar da suka bada a yayin gudanar da kamfe da kuma zabe.
Kungiyar ta bayyana haka ne a cikin wani jawabin da ta fitar a ranar Asabar na taya zababben shugaban kasar, Ahmed Bola Tinubu, da kuma zababben mataimakinsa, Kashim Shettima, murnar samun nasara da suka yi a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gabata.
A cikin jawabin, wanda aka fitar a maimakon Amirah ta kungiyar ta kasa Hajia Rafiah Sanni, ta ma taya hukumar zabe ta kasa murna aiwatar da zaben da ta yi cikin nasara, inda suka bukaci jam'iyyun siyasa da 'yan takara wadanda ba su amince da sakamakon zaben ba, su kai koken su kotu.
Kungiyar ta FOMWAN kuma ta kuma kara da yin kira ga 'yan siyasa da su gujewa kalamai wadanda za su iya haifar da yamutsi a cikin kasa.
Post a Comment