Header Ads

Kasar Sin ta bude kan iyakokinta ga duka matafiya

Shugaban kasar Sin, Xi Jinping

Kasar Sin, wato China, a ranar Talata ta bayyana cewa ta bude duka iyakokinta bayan kasancewarsu cikin tsauraran matakai tsawon shekaru uku sakamakon annobar korona.

Ma'aikatar Kasashen Wajen kasar wadda ta bayyana hakan a cikin wani jawabi, ta ce "Duk wata kalar biza yanzu za a bayar da ita yanzu" zuwa ranar Laraba. 

Dama kasar Sin din ta bude bodar ta cikin watan Janairu domin 'yan kasuwa da kuma iyalai masu kawo ziyara. 

Yanzu masu zuwa yawan bude ido za su iya shiga kasar ba tare da wata matsala ba, a yayin da a wasu yankunan ma ana kokarin gyara abubuwa domin zuwa ba dole sai da biza ba.

Kamar yadda ya ke a cikin jawabin, bizar da aka bayar a da kafin a kulle bodar a ranar 28 ga watan Maci na shekarar 2020, za a iya amfani da su.

No comments

Powered by Blogger.