Header Ads

Karancin naira na iya haifar da ciwon kwakwalwa a tsakanin 'yan Nijeriya - wani masani

  Mista Ben Arikpo

Mista Ben Arikpo, wanda shi ne shugaban Cibiyar Horo da Cigaban Kwakwalwa, ya bayyana damuwarsa dangane da lafiyar kwakwalwar 'yan Nijeriya sakamakon cigaba da fuskantar karancin naira da kuma wasu abubuwan.

Arikpo ya bayyana haka ne a yayin da ya ke tattaunawa da hukumar dillancin labaru ta Nijeriya (NAN) ta wayar tarho a ranar Lahadi a Abuja.

Ya bayyana cewa bude bankuna da ake yi a ranar Lahadi da Asabar abu ne mai kyau, inda ya ce yana da kyau a dage sosai domin a kawo karshen wahalhalun da jama'a ke yi yayin bin layi domin samun kudi da kuma rashin aiki da bankuna ke kasancewa ba su yi a wani lokaci.

Ya bayyana cewa yana da kyau a yi aiki tukuru domin ganin mutane suna samun kudade ba tare da bin layi ba a tsawon rana, inda ya ce rashin kudade na kara yawan wahalhalun da 'yan Nijeriya masu matsakaitan karfi ke fuskanta, wanda ya ce hakan na iya shafar lafiyar kwakwalwa.

"Akwai karuwar nazari a kan lafiyar kwakwalwa a duniya kuma karfin matsalar ya dogara ne a kan me ke haifar da ita.

"Dan Nijeriya mai matsakaicin karfi akwai abubuwa da dama da ya ke fuskanta wadanda suka hada da karancin mai, karancin kudi, tsadar abubuwa da sauransu. 

"In ka gina gidan ka, misali, ka haka ramin burtsatse (borehole), ka sayi falwaya, ka sayi mita da sauransu.

"Ranar da ba ka biya kudin wuta ba za a yanke wutar su ce wadannan kayan nasu ne.

"Irin wannan damuwa ta yi wa mutanen Nijeriya yawa, inda suke haifar da damuwa da sauran abubuwan da ke biyo mata wadanda suna da hatsari ga lafiyar kwakwalwa." Kamar yadda masanin mai suna Afikpo ya bayyana.

"Sai dai kuma cikin rashin sa'a, ba a cika damuwa da rashin lafiyar kwakwalwar 'yan kasa ba. 

"Wannan wani bangaren lafiya ne da ya ke da matukar muhimmanci mu kula da shi domin yana da dangantaka da samun nasarar mu baki daya." Kamar yadda ya bayyana.

Ya bayyana cewa abu ne mai matukar muhimmanci gwamnati ta samar da tsare-tsare wadanda za su tseratar da mutane daga cututtukan kwakwalwa.

Masanin kwakwalwar ya bayyana cewa a 'yan kwanakin baya wasu bankuna guda biyu a Amurka sun rushe kuma sai da gwamnatin Amurka ta shigo ciki domin biyan basukan bankunan.

Ya ce matakin gwamnatin ta Amurka ya sa mutane sun cigaba da kasancewa da ma'ajiyarsu a bankunan ba tare da samun matsaloli sosai ba.

No comments

Powered by Blogger.