Header Ads

Kalaman Jonathan ga Obasanjo yayin taya shi murnar cika shekaru 86


Tsohon shugaban kasar Nijeriya, Dakta GoodLuck Jonathan, ya taya tsohon shugaban kasar Nijeriya, Olusegun Obasanjo, murnar cikarsa shekaru 86 a cikin wani sako da ya yi zuwa gare shi.

Jonathan ya yi wa tsohon shugaban kasar fatar samun tsawon rayuwa a yayin da ya ke aiki domin samar da hadin kai da kasancewar Nijeriya mai cigaba.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana Obasanjo a matsayin dan kasa na nagari, wanda ya cigaba da yin aiki tukuru domin samar da zaman lafiya, daidaito da cigaba ga Afirka.

A cikin sakon taya murnar wanda Jonathan din da kansa ya sawa hannu, ya bayyana cewa, "A madadi na da iyali na, ina taya ka murnar cika shekaru 86 a duniya.

"Ranka ya dade, ka yi rayuwa ta biyayya, aiki da kishi ga Nijeriya da Afirka, samar da hanyoyi na dinke duk wata baraka da kuma tabbatar da zaman lafiya.

"Ina cikin farin ciki matuka ganin cewa duk da shekarun tsufa sun zo, amma kana aiki tukuru domin samar da zaman lafiya a Nijeriya da kuma samar da Afirka mai cike da cigaba.

" A yayin da ka ke cigaba da yin wannan biki, ina yi ma ka fatar samun karfi, ingantacciyar lafiya da kasancewa cikin zaman lafiya. A madadi na da iyalai na, ina yi ma ka barka da ranar haihuwar ka, ranka ya dade." Kamar yadda ya bayyana.

No comments

Powered by Blogger.