Header Ads

Kakakin Majalisar Jihar Yobe Ya Rasa Kujerarsa


Daga Ibraheem El-Tafseer 

Kakakin Majalisar Jihar Yobe Alhaji Ahmed Mirwa na jam'iyar APC ya rasa kujerarsa a zaben gwamnoni da na 'yan majalisun jiha da aka gudanar a jiya Asabar 18 Maris 2023.

Lawan Mirwa shi ne ya ke wakiltar Nguru II (Nguru Outside) a Majalisar Jihar Yobe, tun daga shekarar 2003, ya shafe shekaru 20 a kan wannan kujera kenan. Amma ya fadi a wannan zabe, inda dan takarar jam'iyar PDP, Musa Lawan Majakura ya yi nasara. 

Majakura na PDP ya samu kuri'u 6,648. Mirwa na jam'iyar APC kuma ya samu kuri'u 6,466. Jatau na jam'iyar NNPP ya samu kuri'u 23. Mai Zare na jam'iyar APM ya samu kuri'u 14. Sai Isah Saidu Shehu na jam'iyar ADC ya samu kuri'u 30.

Shugaban tattara sakamakon zabe na Nguru II, Alhaji Mahdi Damaturu ne ya bayyana sakamakon zaben, inda Lawan Musa Majakura na jam'iyar PDP ya lashe zaben. 

Majakura mai shekaru 29, yana da matakin karatu na Diploma, wadda ya yi ta Atiku Abubakar College of Legal and Islamic Studies.

No comments

Powered by Blogger.