Kada ku taka a kasa domin ni, ku yi min addu'a a maimakon haka - Alhaji Abba Yusuf ga magoya bayansa
Zababben gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Yusuf, ya nemi magoya bayansa da mambobin jam'iyyar NNPP da su fasa tunanin "takowa a kasa domin nasara" da ya yi, a maimakon haka su yi masa addu'a domin samun nasara a shugabanci mai zuwa da zai yi.
Abba Yusuf, wanda ya yi takara a karkashin jam'iyyar NNPP, ya lashe zaben na gwamna da aka gudanar a jihar Kano ne da kuri'u 1,019,602 a yayin da babban abokin takararsa na jam'iyyar APC, Gawuna, ya samu kuri'u 890,705.
Zababben gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Laraba a Kano ta bakin kakakin kungiyar kamfe din jam'iyyar NNPP, Sanusi Tofa.
Addu'o'in, kamar yadda Yusuf ya bayyana, sun isa su nuna goyon baya da kuma murnar yin nasarar sa a yayin zaben da aka gudanar ranar Asabar a maimakon takowa a kasa mai tsawo daga wasu manyan masu goyon bayansa, musamman in an yi la'akari da rashin tsaro inda masu garkuwa da mutane, 'yan bindiga da ta'addanci ke yin barazana ga tafiye-tafiyen mutane da kayayyaki hankali kwance daga bangarorin da dama a fadin kasar nan.
Zababben gwamnan ya bayyana aniyarsa ta habaka kayayyakin more rayuwa da samar da walwala ga tsofaffi, ma'aikatan gwamnati da bangaren 'yan kasuwa da sauransu da ke jihar.
"Gwamnatin jihar Kano mai zuwa za ta mayar da hankali ne kan kyakkyawar makoma ga mutane, tsaro, lafiya, ilimi, tattalin arzuki, kayayyakin more rayuwa, samar da walwala ga tsofaffi, ma'aikatan gwamnati, 'yan kasuwa da sauransu." Kamar yadda ya bayyana.
Zababben gwamnan ya bayyana cewa sai an hada hannu domin tabbatar da manufar Kwankwasiyya da kuma mafarkin jam'iyyar NNPP domin samar da kyakkyawan shugabanci wanda zai yiwa jihar aiki baki daya.
Post a Comment