Kada ka ba 'yan Nijeriya da Afirka kunya - Ooni na Ife ga Tinubu
Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi II, ya bukaci zababben shugaban kasar Nijeriya, Ahmed Bola Tinubu, da ya dawo da fata wadda 'yan Nijeriya ke da ita a cikin zuciyoyinsu, inda ya roke shi da kada ya ba mutanen Nijeriya da na Afirka kunya.
Sarkin ya bayyana haka ne a cikin jawabin sakonsa na taya murna ga zababben shugaban kasar wanda darakta a bangaren yada labaru da hulda da jama'a, Otumba Moses Olafare, ya bayyana a fadar ta Ooni din.
Ooni na Ife, wanda har wa yau shine shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta Nijeriya (NCTRN) ya bukaci zababben shugaban da ya kafa kwamiti na mutane hazikai wadanda za su yi kyakkyawan tsari ga tattalin arzukin kasa.
Sarkin ya nemi Tinubu da ya fara aiki nan take da zarar an rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2023 yadda zai tabbatar wa 'yan Nijeriya da "sabuwar fata."
"A matsayin ka na shugaba mai kula sosai a kan yadda abubuwa ke tafiya kuma wanda ake da yakinin zai iya kula da albarkatun wannan kasa har ta kai ga nasara a cikin sauran kasashen duniya, ka da ka ba mutanen Nijeriya da 'yan Afirka kunya.
"A matsayinka na shugaba mai hazaka, nan da 'yan kwanaki kadan muna so mu ga kwamiti da ka yi na mutane maza da mata hazikai wadanda za su tsara mana yadda tattalin arzuki zai kasance domin 'yan Nijeriya na da matukar bukatar fita daga cikin matsin tattalin arzuki da suka tsinci kan su a ciki a 'yan kwanakin nan."
Sarkin ya bayyana cewa saboda "samun sabuwar fata" 'yan Nijeriya suka zabi sabon shugaban kasar, saboda haka da zarar an rantsar da shi ya fara aiki ba tare da bata lokaci ba domin tabbatarwa 'yan Nijeriya akwai "sabuwar fatar."
Post a Comment