Header Ads

Jirgin saman Nigeria Air zai fara aiki kafin 29 ga watan Mayu - Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa jiragen sama mallakin Nijeriya, Nigeria Air, za su fara gudanar da cikakken aiki kafin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta zo karshe.

Ministan jiragen sama, Hadi Sirika, ne ya bayyana haka a yayin wani taro na masu ruwa da tsaki a cikin harkokin jiragen sama a Abuja a ranar Alhamis.

A yayin da ya ke amsa tambayar yaushe ne takamaimai jiragen saman za su fara aiki, sai ya ce, "Kafin karshen wannan gwamnatin, kafin 29 ga watan Mayu, za su tashi."

Ministan ya kara da cewa gwamnatin tarayya za ta bar sashen na jiragen sama da kyau fiye da yadda ta same shi domin ta cimma akalla kaso 90 cikin 100 na shirye-shiryen ta a kansa. 

Ministan ya tabbatarwa kamfanonin jiragen sama cewa makalewar kudadensu zai zama tarihi, domin ya iya kokari domin kamfanonin su fahimci kowanne hali da ake ciki, kuma gwamnati tana aiki domin sakin duk wasu kudade da suka makale nan take.

Yayin da ya ke magana a kan tsaron rayuka, Darakta Janar na sabuwar hukumar kula da tsaron rayukan jama'a a Nijeriya da aka kafa, Akin Olateru, ya bayyana ayyukan hukumar wajen hana afkuwar hadurra.

No comments

Powered by Blogger.