Jam'iyyar APC ta ɗauki manyan lauyoyi 13 domin yin kariya ga nasarar Tinubu a kotu
Jam'iyya mai mulki ta APC a ranar Talata ta samar da wata tawagar kwararrun lauyoyi domin samar da kariya ga nasarar Tinubu a kotun shari'ar zaben shugaban kasa.
Wannan na kunshe ne a cikin wani jawabi wanda mai ba jam'iyyar shawara ta bangaren shari'a na kasa, Ahmad El-Marzuq, ya bayyana.
Kamar yadda ya bayyana, tawaga ce ta kwararru a bangaren shari'ar da ta shafi zabe, dokar tsarin mulki da sauran abubuwan doka da shari'a.
Wannan tawaga ta kwararrun lauyoyi masu matsayin SAN, Prince Lateef Fagbemi, wanda ya ke sanannen lauyan, shi zai jagorance ta.
Kamar yadda El-Marzuq ya bayyana, Fagbemi ya sha yin shari'o'i wadanda suka shafi zabe da sauran manyan shari'o'i daban-daban.
Ya bayyana kwarin gwaiwar da ya ke da shi na cewa tawagar na da kwarewa da karfin da za ta iya kaiwa ga nasarar jam'iyyar ta APC a kotun shari'ar zaben shugaban kasar, inda ya yi kira ga duka mambobin jam'iyyar ta APC su goyi bayan tawagar domin ganin abinda mutane suka zaba a zaben da ya gudana na 25 ga watan Fabrairu sun same shi.
Sai ya kara da kira ga duka wasu mutane da wannan abu ya shafa su yi komai cikin kwarewa da kuma bin doka.
Kwararrun lauyoyin dai sune Lateef Fagbemi (jagoransu), Ahmad El-Marzuq, Sam Ologunorusa, Rotimi Oguneso, Olabisi Syebo, Gbotega Oyewole, Muritala Abdulrasheed, Aliyu Saiki, Tajudeen Oladoja, Pius Akubo, Oluseye Opasanya, Suraja Saidai da kuma Kazeem Adeniyi.
Post a Comment