Jami'an NDLEA sun kama kwayoyin Tramadol miliyan 1.2 a jihohin Kogi da Gombe
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA a yayin wasu ayyuka guda biyu da ta gudanar a jihohin Kogi da Gombe ta kama kwayoyin opioids miliyan daya da dubu dari biyu da dubu biyar da dari biyu da sittin (1,205,260).
Daraktan watsa labarun hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi.
A yayin da ya ke yin bayani daki-daki kan yadda ayyukan hukumar ya kasance, Babafemi ya bayyana cewa a jihar Kogi, kwayoyin Tramadol 530,160 da kuma kwayoyin diazepam 99,000 aka kama a kan titin Okene zuwa Abuja daga wani direban bas mai suna Suleiman Oyedekun dan shekara 41, wanda ya taso daga garin Onitsa daga jihar Anambara zai tafi Kontagora da ke jihar Neja a ranar Litinin, 13 ga watan Maci.
A ranar kuma, kwayoyin Tramadol 576,100 wadanda aka zuba cikin wata jaka da ke dauke da takalman silifas jami'an hukumar ta NDLEA ta kama a wani garejin manyan motocin tirela da ke titin Old Mile a garin Gombe, karamar hukumar Akko da ke jihar Gombe, an kuma kama mutane hudu da ake zargi yayin kama kwayoyin, mutanen sune Usman Suleiman, Ya'u Yusuf, Saidu Suleiman da kuma Abubakar Umar.
A jihar Kaduna, kilo 367 na cannabis sativa aka kama a cikin wata mota mai lamba FKJ141DX.
Dangane da hakan, an kama mutane biyu da ake zargi, Monday Suleiman dan shekara 62 da Sama'ila Mohammed dan shekara 30 a yayin da kuma cin hanci na naira miliyan daya da dubu dari biyu (1,200,000) da aka ba jami'an hukumar ta NDLEA aka rubuta shi cikin kayan da aka karba daga hannun mutanen da ake zargi.
Haka kuma a ranar Laraba, 15 ga watan Maci, jami'an hukumar NDLEA sun kama wata mata mai tace Cannabis Sativa da kuma dry gin mai suna Ebi Akpotudua mai shekaru 52, inda ta ke hada wani abin sha mai suna Monkey tail. An kama ta ne a Ugboroke kusa da River Road, da litocin abin shan na Monkey tail har 19.5 da kuma Cannabis mai nauyin kilo 22.2.
Ciyaman ko kuma shugaban sashen zartarwa na hukumar ta NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya, ya yi yabo sosai ga jami'an hukumar na yadda suka kasance a natse a kan aikinsu da kuma yadda suka nuna kwarewa.
Post a Comment