Header Ads

Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Sin da Rasha sun fara atisayen sojojin ruwa a Tekun Oman

Wani jirgin ruwan yaki mallakar Jamhuriyar Musulunci ta Iran

Kasashen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Sin da Rasha sun fara gudanar da atisayen sojojin ruwa na hadin gwiwa a Tekun Oman, a yayin da kasashen ke yunkurin kara karfafa dangantaka a tsakanin sojojinsu na ruwa.

Atisayen, wanda a turance aka yiwa lakabi da "naval security belt combine war game 202" an fara shi ne a ranar 15 ga watan Maci kuma zai cigaba har zuwa ranar 19 ga watan Maci kamar yadda ma'aikatar tsaron Sin ta bayyana a cikin wani jawabi a ranar Laraba.

Atisayen zai samar da "yin aiki a aikace na hadin gwiwa a tsakanin kasashen da ke yinsa" kamar yadda ya ke a cikin jawabin.

Wannan atisaye dai zai hada da bangarori da dama na sojojin ruwan kasar Iran.

Sojojin ruwan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, da na kasar Sin da takwarorinsu na kasar Rasha sun sha yin atisayen sojojin ruwa a cikin 'yan shekarun nan da nufin kara tabbatar da tsaro ga safarar kasa-da-kasa da ake yi ta tekuna, hana fashi da ta'addanci a cikin tekuna, samar da bayanai ga juna wajen yin ceto da taimako ga sojojin ruwa da kuma samar da dabaru ga juna a yayin aiki.

No comments

Powered by Blogger.