Header Ads

Isra'ila ta kai sabon hari a filin saukar jiragen sama na kasa-da-kasa da ke Aleppo a Siriya


Wani hoto na harin da Isra'ila ta kai a filin jirgin sama da ke Aleppo

Siriya ta yi Allah wadai da sabon harin da Isra'ila da kai kasar, wannan karon a filin jiragen sama na kasa-da-kasa da ke arewa maso yammacin Aleppo, inda ta bayyana harin da karya dokokin kasa-da-kasa ne.

Ma'aikatar Harkokin Kasashen Wajen ta Siriya ta bayyana cewa harin na kara yin nuni ne da irin rashin bin ka'ida da rashin wayewa da kuma rashin mutunta bil-adama na Tel Aviv, kamar yadda kafar watsa labarun kasar, SANA ya ruwaito. 

Ma'aikatar ta bayyana harin da cewa laifi ne biyu, domin hari ne a filin jirgin sama na farar hula kuma an yi shi ne kan wurin da ake shigo da kayan jin kai ga wadanda ibtila'in girgizar kasar 6 ga watan Fabrairu ta shafa.

Harin dai Isra'ila ta yi shi ne da sanyin safiyar ranar Talata a kan filin jiragen sama na kasa-da-kasa da ke Aleppo daga bangaren Tekun Meditaraniya, yammacin birnin gabar ruwa na Latakia, inda harin ya sa ayyukan filin jirgin suka tsaya tsak.

Kafofin watsa labarun Siriya sun bayyana cewa Siriya ta yi nasarar kabo wasu daga cikin makamai masu linzami da Isra'ilan ta harbo daga yankin tekun na Meditaraniya, inda Siriyan ta gargadi Isra'ila ta guji irin abinda zai afka mata sakamakon irin wadannan dabi'u tare da yin kira ga kasashen duniya da su dauki duk matakin da ya dace domin kawo karshen laifuffuka da Isra'ila ke aikatawa.

No comments

Powered by Blogger.