Header Ads

Isra'ila ta fuskanci zanga-zanga mafi girma a cikin tarihin ta

Kafofin yada labarun Isra'ila sun bayyana cewa mutane 500,000 suka fito kan tituna domin gudanar da zanga-zanga da suka kira mafi girma a tarihin kasar.

A babban birnin kasar, Tel Aviv, kimanin mutane 200,000 suka gudanar da zanga-zanga rike da tutar kasar.

'Yan kasar Isra'ila din dai suna gudanar da zanga-zangar ne domin nuna adawa da shirin gwamnatin kasar na yin sauye-sauye a bangaren shari'ar kasar.

Firaministan kasar ta Isara'ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa sauye-sauyen - wadanda za su rage karfin ikon da kotunan kasar ke da shi - za su taimaka wajen daidaita iko tsakanin bangarorin gwamnati, sai dai 'yan adawa na kallon matakin da baraza ga tsarin damakaradiyya. 

A cikin daya daga zanga-zangar da ya jagoranta, shugaban adawa na kasar, Yair Lapid, ya ce wannan "babbar barazana ce ga kasar."

Wannan zanga-zanga dai da ake yi a Isra'ila ta shiga cikin sati na 10 kenan, kuma masu zanga-zangar sun sha alwashin cigaba da yin ta har in majalisar kasar ba ta dakatar da dokar ba. A Tel Aviv da wasu wuraren zanga-zangar kan rikide ta koma fada a wasu lokutan.

No comments

Powered by Blogger.