Header Ads

Isra'ila na da 'yancin kai hari ma'aikatar nukiliyar Iran domin kare kan ta Cewar Netanyahu zuwa ga shugaban IAEA


Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana kalaman shugban hukumar kula da shirin nukiliya ta duniya (IAEA), Rafael Grossi, da kalamai "wadanda ba su dace ba" da ya ke cewa duk wani harin soja kan ma'aikatun nukiliyar Iran ba za su kasance kan ka'ida ba.

A dai ranar Asabar ne shugaban hukumar sa idon ta majalisar dinkin duniya ya ce duk wani harin soja a kan ma'aikatun nukiliyar Iran "ba zai kasance kan ka'ida ba" kuma "haramtacce" a yayin da ya ke mayar da martani ga barazanar kasashen Amurka da Isara'ila da ke kokarin kai masu hari.

"Ina tunanin duk wani hari, duk wani hari na soja a kan ma'aikatun nukiliya haramtacce ne, wannan wani abu ne da duk muka yarda da shi." Grossi ya bayyana yayin wani taro da ya yi da shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran, Mohammad Eslami, a Tehran.

Wadannan kalamai na zuwa ne a yayin da rahotanni ke nuna cewa gwamnatin Biden ta kara kusanci da kasar Isra'ila tare da yin manya-manyan atisayen soji bayan an kasa cimma matsaya yayin da aka tattauna kan shirin makamashin nukiliyar na Iran.

"Rapael Grossi mutum ne mai yin abubuwan da suka dace amma ya yi kalaman da basu dace ba." Netanyahu ya bayyana yayin wata ganawa da ya yi da wasu 'yan majalisarsa masu tsatstsauran ra'ayi a ranar Lahadi. 

"Ba kan ka'ida ba a wace dokar? Kan ka'ida ne ga Iran wadda a fili ta ke neman ganin karshenmu ta kera makamai domin ganin karshenmu? An hana mu ne mu kare kan mu? A fili ya ke za mu yi hakan." Firaministan ya bayyana.

A cikin watan da ya gabata, Ambasadan Amurka a Isra'ila, Tom Nides, ya bayyana cewa "akwai zabi daban-daban" wanda kowanne za a iya yin amfani da shi a kan Iran, kuma Isra'ila "za ta iya yin duk abinda ta ga dama ta yi kuma muna goyon bayanta."

Isra'ila, wadda ta mallaka makaman nukiliya kuma ta ki sa hannu a cikin dokar hana yaduwar makaman nukiliyar, ta yi shirye-shirye da dama a 'yan shekarun nan na yin zagon kasa ga shirin makamashin nukiliyar Iran wanda ya ke na zaman lafiya ta hanyar kashe masu ilimin kimiyya a Iran da kuma yin hare-hare a kan ma'aikatun nukiliyar Iran. 

Bayan haka, sau da dama Isra'ila ta yi barazanar kai hare-hare a kan ma'aikatun na nukiliyar Iran, inda ta ke ikirarin cewa Iran na gaf da kera makaman nukiliya.

Duk wannan na zuwa ne kuwa duk da cewa Iran ta nunawa duniya cewa shirin nukiliyar ta na zaman lafiya ne ta hanyar sa hannu a cikin yarjejeniyar JCPOA a shekarar 2015 tare da manyan kasashen duniya guda shida - Amurka, Jamus, Faransa, Birtaniya, Rasha da kasar Sin. Iran na bin kowacce ka'ida da ke cikin yarjejeniyar JCPOA har sai shekarar 2019, a lokacin da Amurka ta janye kanta daga yarjejeniyar sakamakon matsin lamba daga Isra'ila, tare kuma da kara kaimi wajen takurawa ga Iran.

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ma sa hannu a yarjejeniyar NPT kuma ta hana samarwa, mallaka ko amfani da makaman nukiliya sakamakon fatawa daga shugaban juyin-juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei.

No comments

Powered by Blogger.