Header Ads

Isra'ila da Ingila na cikin damuwa sakamakon sake kulla dangantaka tsakanin Iran da Saudiyya - Tehran

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu tare da Firaministan Ingila, Rishi Sunak

Kasar Iran ta yi watsi da zarge-zargen Isra'ila da Ingila a kan shirin makamashinta na nukiliya da kuma irin rawar da ta ke takawa a yankin, inda ta bayyana cewa kasashen biyu suna cikin damuwa ne sakamakon sake kulla dangantaka a tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasar Saudi Arabiya.

Wadannan kalamai na zuwa ne daga kakakin Ma'aikatar Kasashen Waje ta Iran, Nasser Kan'ani a ranar Asabar, bayan Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, da takwaransa na Ingila, Rishi Sunak, sun zargi Iran da "yin ayyukan da ke haifar da rashin daidaituwa" a yayin tattaunawarsu ranar Juma'a a Landan. 

"Wani abu ne sananne cewa wadannan kasashe guda biyu dama suna yin zarge-zarge ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wadda ke kokarin samar da daidaituwa a yankin." Kamar yadda Kan'ani ya bayyana.

"Daya daga cikin wadannan kasashe ta dogara ne da mamaye wata kasa domin ta rayu, kuma a kodayaushe ayyukanta shine aikata laifuffuka da kashe kananan yara kuma ta ki shiga cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT) a yayin da ita kuma daya kasar irin tsare-tsaren ta da ke tunzura afkuwar yaki da kuma dabi'u da ke haifar da bore ana iya ganinsu a ko'ina." Kamar yadda Kan'ani ya bayyana.

"Idan mun yi la'akari da yadda wadannan kasashe suke da kuma yin duba da irin yadda ake samun cigaban abubuwa a wannan yanki, ba abun mamaki ba ne su kasance cikin damuwa da bakin ciki a kan yadda abubuwa ke tafiya a yankin kuma su yi kokarin raunata abubuwa su kuma kawo karshensu." Kamar yadda kakakin ya bayyana.

Kan'ani na magana ne dangane da gagarumar yarjejeniya da aka cimmawa a farkon wannan watan a tsakanin Iran da Saudi Arabiya ta sake dawo da dangantaka a tsakani bayan tsawon shekaru bakwai. Masana na da ra'ayin cewa dawo da dangantaka a tsakanin Tehran da Riyadh zai kawo karshen fadace-fadace a yankin yammacin nahiyar Asiya.

"Iran na kara jaddada cewa tana daukar karfafa dangantaka da makwaftanta da matukar muhimmanci." Cewar Kan'ani.

Kamar yadda kakakin ya fada, Iran na jaddada cewa za a iya samun tsaron yankin ne kawai idan kasashen yankin suka hada kansu.

Kamar yadda wani jawabi da ofishin Netanyahu ya nuna, tattaunawarsu a Landan ta mayar da hankali ne a kan yadda za a samar da wata hadaka domin tsayar da shirin nukiliyar kasar Iran.

Ofishin firaministan Ingila, Downing Street, ya bayyana cewa tattaunawar tsakanin Benjamin Netanyahu da Sunak sun mayar da hankali ne kan yakin kasar Ukraine, ayyukan Iran a yankin da kuma shirinta na makamashin nukiliya da kuma "karfafa dangantaka a bangaren saro, leken asiri da tattalin arzuki" a tsakanin Isra'ila da Ingila.

Kan'ani ya tabo "duka laifuffuka na yau da kullum da keta hakkokin bil-adama da dokokin kasa-da-kasa na gwamnatin Isra'ila" inda ya yi tunatarwa a kan nauyin da ya hau kan kasashen duniya da ke goyon bayan Isra'ila.

No comments

Powered by Blogger.