Header Ads

Iran za ta cigaba da kare hakkokin mata duk da takunkumin da Amurka ta sanya wa kasar - Zahra Ershadi


Mataimakiyar wakilin kasar Iran a majalisar dinkin duniya, Zahra Ershadi

Mataimakiyar wakilin kasar Iran a majalisar dinkin duniya, Zahra Ershadi, ta bayyana cewa kasar Iran za ta cigaba da kasancewa mai tabbatar da cewa mata sun samu cigaba tare da kare hakkokinsu duk da wahalhalu wadanda takunkumin Amurka wadanda ba kan ka'ida suke ba suka haifar.

A yayin da ta ke yin jawabi yayin wata muhawara a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya a kan mata, zaman lafiya da tsaro, Zahra Ershadi ta bayyana cewa Tehran ta yi imanin a kodayaushe za a iya samar da cigaba da kuma tabbatar da hakkoki ga mata.

A yayin muhawarar ta ranar Talata, wakiliyar Amurka a majalisar dinkin duniya, Linda Thomas-Greenfield, ta yi ikirarin cewa mata da yara 'yan mata a Iran suna fuskantar cin zarafi, wasu ma kasashen yamma duk sun yi irin wadannan zarge-zarge.

Zahra Ershadi ta bayyana cewa Iran tana kalubalantar duk wani jawabi da aka yi kan kasar wanda bai kamata ba da wasu kasashe suka yi. 

"Mata a Iran suna taka rawa a kowanne fanni, bangaren kimiyya, ilimi, siyasa kuma suna taka muhimmiyar rawa a cikin rayuwar al'umma." Ta bayyana, inda ta nuna damuwa game da wasu matakai a kan mata da gwamnatin Afghanistan ta Taliban ta dauka a kan mata.

Ta bayyana cewa wasu kasashen sakan yi amfani da dokokin duniya da kuma hakkin bil-adama domin cimma muradansu na siyasa, kuma su yi amfani da majalisar dinkin duniya domin su cimma manufofinsu, amma kuma sai su yi shiru yayin da ake cin zarafi da take hakkokin mata wanda Isra'ila ke yi ga mata da 'yan mata na Falasdinawa.

"Irin kasashen nan su kan goyi bayan dokokin Isra'ila na wariyar launin fata ko kunya ba su ji da sunan kare kan ta, su kuma kawar da kansu daga tursasawa da wahalhalun mata Falasdinawa. Irin wadannan tsare-tsare na siyasa za su iya kawar da mutuncin majalisar dinkin duniya." Kamar yadda wakiliyar ta bayyana.

No comments

Powered by Blogger.