Iran ta nemi a cire wa Siriya takunkumin da aka kakaba mata
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kira da a cire duk wani takunkumi da yammacin duniya suka kakabawa Siriya ba tare da sharadi ba domin ta samu saukin samun taimako a dalilin girgizar kasa da kasar ta fuskanta a farkon watan Fabrairu.
Ambasadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a majalisar dinkin duniya, Ameer Saeed Iravani, ne ya bayyana haka ga kwamitin tsaro na majalisar kan al'amarin a yankin Gabas ta Tsakiya a ranar Talata.
Ibtila'in girgizar kasar wadda ta shafi kasar ta Siriya da makwafciyarta Turkiyya, zuwa yanzu ta yi sanadiyyar rasa ran mutane sama da 50,000 a kasashen biyu.
Iravani, wanda ya bayyana cewa al'amarin girgizar kasar ta kara sa abubuwa sun ta'azzara ga jama'a inda sukan rasa abubuwan da bil-adama ke bukata domin rayuwa, ya bayyana cewa, "Idan muka yi la'akari da yadda wannan girgizar kasa ta sa abubuwa suka ta'azzara, dole a samar da taimakon gaggawa ba tare da sa siyasa ko sharadi ga mutanen da ke bukatar taimakon ba.
"Domin a tabbatar da samar da agajin na gaggawa, dole kasashen duniya su mayar da hankali wajen cire takunkumi na rashin mutuntaka da aka kakaba."
Kasar Siriya ta kasance wata kasa da kasashen yammacin duniya suke ta kakabawa takunkumi tun shekarar 1979. Takunkumin da Amurka ke sanyawa kasar da kawayenta sun kara yawa a shekarar 2011 yayin da kasar ta samu kanta karkashin hare-haren ta'addanci da kasashen waje ke daukar nauyi, sun kuma kara lunkuwa a shekarar 2019 yayin da Amurka ta zartar da dokar Caesar Act wanda ke nufin duk wani mutum da ya yi hulda da Siriya din kai tsaye ko ba kai tsaye ba wajen sake gina ta takunkumi zai shafe shi.
Ambasadan ya tunatar cewa irin wannan takunkumi karya dokar kasa-da-kasa ne kuma karya dokar majalisar dinkin duniya ne, inda ya bayyana cewa akwai bukatar a yi aiki domin samar da taimako ba jajantawa kawai ba.
Ambassadan Jamhuriyar ta Musulunci ya kuma yi Allah wadai da hare-haren da Isra'ila ta kai a Siriya din a ranar 9 ga watan Fabrairu a birnin Damaskus wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 5 cika har da soja daya, wasu 15 kuma suka samu mummunan rauni.
Iravani ya bayyana hare-haren da barazana ne ga zaman lafiyar yankin tare da yin kira ga kasashen duniya da su dakatar da Isra'ila daga rashin mutunta iyakokin Siriya da ta ke yi.
Post a Comment