INEC ta yi amfani da wata na'ura ta uku domin murguda sakamakon zabe saboda samun nasarar Tinubu - Atiku
Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya zargi hukumar zabe mai zaman kan ta, INEC, da kafa wata na'ura ta uku domin "murguda" sakamakon zaben ranar 25 ga watan Fabrairu saboda dan takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya yi nasara.
Atiku ya yi wannan ikirari ne a cikin wani kundi mai shafuka 66 ma lambar kara :PEPC/A/05/2023 wanda kara ce da aka shigar a gaban kotun da ke sauraron kararrakin da suka shafi zaben shugaban kasa (PEPC) da ke kotun Appeal da ke Abuja.
Atiku da PDP sune suka shigar da kara a yayin da hukumar INEC, Tinubu da jam'iyyar APC sune aka shigar kara na daya, na biyu da na uku.
A cikin karar, masu kai karar sun bayyana cewa suna son su nuna hujjojin cewa ba kamar yadda aka tsara na'urar BVAS ba na ta loda sakamakon zabe kai tsaye zuwa na'urar tattara alkaluman zabe ba a shafin IReV, wanda ake kara a farko (hukumar INEC) ta kafa wata na'ura (Device Management System) wadda asalin aikin na'urar shine samar da tsaro ga fasahar INEC, amma a zaben shugaban kasa aka yi amfani da ita domin tarbe sakamakon zabe, ta killace shi, ta ajiye shi ta kuma tace shi kafin ta tura zuwa shafin IReV.
Karar ta yi ikirarin cewa wanda ake kara na farko ya yi amfani da wannan na'ura domin murguda sakamakon zabe da samun nasarar wanda ake kara na biyu da na uku.
Dan takarar jam'iyyar ta APC, Tinubu, an bayyana shi ne a matsayin wanda ya yi nasara a jihohi 12 cikin 36 na Nijeriya, kuma ya samu kuri'u da dama a cikin sauran jihohin inda ya samu kuri'u 8,794,726, shi kuma dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku, wanda a yanzu ya ke neman kujerar shugaban kasa sau shida kenan, ya samu kuri'u 6,984,520, sai kuma na jam'iyyar LP, Peter Obi, wanda ya samu kuri'u 6,101,533.
Atiku da Obi dai a yanzu haka sun shiga kotu domin kalubalantar bayyana Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara kuma zababben shugaban kasa.
Post a Comment