INEC ta yi alkawarin yin amfani da na'urar BVAS a zaben gwamnoni
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya (INEC) ta tabbatarwa 'yan Nijeriya cewa za ta yi amfani da na'urar tantance masu zabe ta BVAS a zaben da ke tafe na gwamnoni da 'yan majalisun jiha.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana haka a ranar Asabar yayin wani taro da ya yi da kwamishinon da ke kula da zabe a matakin jiha (REC) a cibiyar hukumar da ke Abuja.
Shugaban hukumar ya tabbatar da cewa an yi aiki a kan na'u'rorin na BVAS domin gujewa matsalolin da aka fuskanta a yayin gudanar da zaben shugaban kasa da kuma 'yan majalisun kasa.
Farfesan, wanda ya bayyana cewa taron an yi shi ne domin yin duba ga zaben da ya gudana a satin da ya gabata, ya ce akwai darussa da za a iya koyo daga zaben musamman wadanda suka shafi shirye-shiryen abubuwa da daukar abubuwa zuwa wurare da sauran tsare-tsare.
Shugaban hukumar sai kuma ya bukaci kwamishinonin zaben da su tabbatar da cewa zaben da ke tafe na gwamnoni bai fuskanci irin matsalolin da aka fuskanta a baya ba kuma a tabbatar da cewa an hukunta jami'ai wadanda ba su bi ka'ida ba.
Post a Comment