Ibtila'in gobara ya yi sanadiyyar konewar wasu kauyuka a jihar Jigawa
Sakamakon wani ibtila'i na gobara da ya afku a cikin karamar hukumar Kiyawa da ke jihar Jigawa da ke arewacin Nijeriya a ranar Lahadi, daruruwan gidaje sun kone tare da yin asarar dukiya mai yawa a wasu kauyuka guda uku.
Gobarar ta faru ne a kauyukan Malamawa, Karangiya da kuma Kwaleji kuma daruruwan gidaje, amfanin gona da dabbobi masu yawa ne suka kone.
Kamar yadda rahotanni suka nuna, an kashi lokaci mai tsawo kafin a iya kashe wutar sakamakon iskar da ke kadawa a kauyukan.
Mutanen kauyukan a bayan gari suka kwana sakamakon konewar da gidajensu suka yi a ibtila'in gobarar.
Post a Comment