Hukumar NDLEA ta kama wakilan jam'iyya da katunan cirar kudi domin sayen kuri'a
A jihar Ogun da ke kudu-maso-yammacin Nijeriya, hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta kama wasu mutane hudu da daruruwan kotunan cirar kudi domin sayen kuri'a.
A cikin wani sako da ta sa a shafin ta na Twitter, hukumar ta bayyana cewa an loda wa kowanne kati 10,000 tare da sa masa lambobin sirri wadanda ake zargin na sayen kuri'a ne.
Post a Comment