Header Ads

Hukumar INEC ta bayyana sakamakon zaben jihar Adamawa a matsayin wanda bai kammalu ba

'Yar takarar gwamna a jam'iyyar APC, Aishatu Dahiru da Gwamnan jihar Adamawa mai takara a jam'iyyar PDP, Ahmadu Fintiri

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana zaben gwamna da aka gudanar a jihar Adamawa a matsayin wanda bai kammalu ba (inconclusive).

Duk da cewa sakamakon zaben da hukumar ta INEC ta nuna ya nuna cewa gwamnan jihar wanda ke takara a karkashin jam'iyyar PDP, Ahmadu Fintiri, ne ke da yawan kuri'u, hukumar ta bayyana cewa kuri'un da aka soke sun fi karfin tazarar da za a iya bayyana nasara a tsakanin Fintiri din da babbar abokiyar takararsa, Aisha Dahiru ta jam'iyyar APC.

Za dai a sanar da sabon lokaci domin gudanar da zabuka a wuraren da ba a iya yin zabukan ba.

A karshen sakamakon da hukumar ta bayar, Fintiri ya yi nasara a kan Aisha da kuri'u sama da 30,000.

Gwamnan ya samu kuri'u 421,524 a yayin da Aisha, wadda aka fi sani da Binani, ta samu kuri'u 390,275.

Gwamna Fintiri ya yi nasara a kananan hukumomi 13 cikin 21 da suke a jihar Adamawa a yayin da Binani ta yi nasara a sauran guda 8.

Sakamakon zaben kamar yadda hukumar ta INEC ta bayar shine:

Mutanen da suka yi rijistar zabe: 2,196,566
Masu zabe da aka tantance: 859,964

AA - 641
ADC - 2996
ADP - 2134
APC - 390,275
APGA - 876
APM - 603
APP - 284
LP - 2729
NNPP - 4847
NRM - 1237
PDP - 421,524
PRP - 1185
SDP - 6865
YPP - 1425
ZLP - 199

Kuri'un da aka kada da kyau: 837820
Kuri'un da ba a kada da kyau ba: 14888
Yawan kuri'un da aka kada: 852708

No comments

Powered by Blogger.