Header Ads

Hamas ta yi zanga-zangar nuna goyon baya ga al-Quds


Jama'a a wurin zanga-zangar da aka gudanar bayan an kammala sallar Juma'a

An gudanar da babbar zanga-zanga a Gaza domin nuna goyon baya ga Falasdinawa da suke a al-Quds da kuma yankin da aka mamaye na yamma da gabar kogin Jordan a yayin da hare-haren mazauna 'yan Isra'ila ke kara ta'azzara a kan Falasdinawa.

Mutane daga kowanne bangare sun nuna aniyarsu ta cigaba da yin fafutika, wadda ita ce hanya mafi dacewa domin samar da kariya ga al-Quds da kuma yamma da gabar kogin Jordan daga hare-haren Isra'ila.

A cikin kwanakin na dai zaman dar-dar ya kara lunkuwa bayan da mazauna 'yan Isra'ila da taimakon sojojin Isra'ila suka fada kauyukan da suke a yankin yamma da kogin Jordan tare da kunnawa motoci da gidaje wuta.

Hamas ta bayyana cewa a wannan wata da ke tafe na Ramadan za a kara kaimi wajen fafutikar kare kai daga gwamnatin ta Isra'ila, inda masu sa ido suka bayyana cewa kasashen duniya sun kasa taimakawa Falasdinawa da ke zaune a yankin da aka mamaye na yamma da gabar kogin Jordan kuma sun kauda fuska daga keta dokoki da Isra'ila ke yi a kansu.

Kamar yadda Hamas ta bayyanawa gidan talabijin din Press TV, Falasdinawa za su kasance a tare domin tunkarar kowacce irin tursasawa daga Isra'ila.

Hare-haren Isra'ila da na mazauna Isra'ila din sun yi sanadiyyar rasuwar mutane saba'in tun farkon wannan shekara ta 2023 a yankin da aka mamaye na yamma da kogin Jordan da kuma al-Quds.

A yayin zanga-zangar, an yi ta rera wakokin nuna kin amincewa da Isra'ila tare da kiran duka musulmai su goyi bayan Falasdinawa kuma su taimaka a samar da kariya ga al-Quds.

No comments

Powered by Blogger.