Header Ads

Gwamnan Kogi ya sha alwashin kamawa da hukunta duk wanda ya ki karbar tsaffin kudi

Gwamnan jihar Kogi

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana cewa gwamnatin sa ba za ta sa ido ana kin karbar tsofaffin kudade ba wanda wasu mutane da 'yan kasuwancin ke yi duk da cewa kotun koli ta halatta cigaba da amfani da su.

Gwamnan ya bayyana cewa kin karbar tsofaffin kudaden rashin bin umarnin kotu ne karara, kuma gwamnatinsa ba za ta amince da hakan ba.

"Duk wanda ya ki karbar tsofaffin kudaden a kai rahotonsa ga jami'an tsaro da hukuma domin a kama sa cikin gaggawa a yanke masa hukunci." Kamar yadda kwamishinan watsa labaru da sadarwa na jihar Kogi, Mista Kingsley Fanwo, ya bayyana a cikin wani jawabi a Lokoja.

Ya ma bayyana cewa za su dakatar da duk bankin da ya ki karbar tsofaffin kudi a jihar, domin ba za su zura ido suna kallon wani banki da ya ki bin umarnin doka ba, kuma ma har dokar kotun koli.

A ranar Larabar satin da ya gabata ne kotun koli ta bayar da umarnin cigaba da yin amfani da tsofaffin takardun N1000, N500 da N200 har zuwa 31 ga watan Disambar 2023.

Duk da cewa wasu bankunan sun fara bayar da tsofaffin kudade ga kwastomominsu, to amma wasu 'yan kasuwa da sauran mutane na cigaba da kin karbar su.

Abinda ya sa kuwa shine babban bankin na Nijeriya da gwamnatin Nijeriya basu fito da gamsasshen bayani cewa a cigaba da karbar tsofaffin kudaden ba.

Sai dai gwamna Yahaya Bello ya bayyana hakan da "abinda ba za a amince da shi ba" kuma "zubar da kima ne" cigaba da kin karbar kudaden duk da cewa kotun koli ta yanke hukunci kan batun su.

Inda ya bayyana cewa a matsayinsu na masu kishin kasa, mutanen Kogi dole su karba, "A matsayinmu na masu kishin kasa, mutanen Kogi dole su karba domin ba za mu kashe tattalin arzukinmu ba bayan kotu ta bamu 'yanci."

"Saboda haka gwamnatin jihar ta samar da kwamiti wanda zai tabbatar da cewa ana bin umarnin kotu dangane da amfani da tsofaffin takardun kudin."

Gwamnan jihar ya yi kira ga duk mutanen jihar ta Kogi da su tabbatar suna karbar tsofaffin kudaden tunda bankunan kasuwanci sun fara bayar da su domin cigaba da gudanar da hada-hadar kasuwanci na yau da kullum.

No comments

Powered by Blogger.