Gwamnan Kano ya yi afuwa ga fursunoni 12 wadanda aka yanke wa hukuncin kisa
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi afuwa ga fursunoni mutum 12 wadanda aka yankewa hukuncin kisa.
SC Musbahu Lawan Nassarawa, wanda shi ne mai magana da yawun gidan ajiya da gyaran hali na jihar, a cikin wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa gwamnan ya yi wa fursunonin afuwa ne saboda cunkoso da ake samu na wadanda aka yankewa hukuncin kisa.
A cikin sanarwar ya bayyana cewa tun a shekarar da ta gabata aka so yi masu afuwa, to amma hakan bai yiwu ba saboda sai da aka dauki lokaci aka tantance su, inda ya bayyana cewa yanzu an samu sauki na yawan wadanda aka yankewa hukuncin kisa a gidajen hari bayan wannan afuwa da gwamnan ya yiwa wasu daga cikinsu.
Wasu mata guda hudu wadanda suka kwashe shekaru a daure su ma sun samu afuwar gwamnan saboda kyakkyawan hali da suka nuna a lokacin da suke daure.
An yi kira ga wadanda suka samu afuwar da su zamo mutane na kirki bayan komawarsu cikin al'umma sannan kuma su guji duk abinda zai sa su komo wannan gida na gyaran hali.
Kamar yadda ya ke a cikin sanarwar, wasu fursunonin da aka yiwa afuwa sun kwashe shekaru 25 suna jiran aiwatar da hukuncin kisa a kan su.
Post a Comment