Header Ads

Gobara ta kara tashi a wata kasuwa da ke jihar Borno

Kasuwar a yayin da take ci

Gobara ta kara tashi a garin Maiduguri da ke jihar Borno, a wannan karon a wata sananniyar kasuwa mai suna Gamborun Market, inda ta kona shaguna masu tarin yawa.

Kamfanin dillancin labaru a Nijeriya wato NAN ya ruwaito cewa wutar, wadda ta tashi a ranar Asabar, ta fara ne da karfe 2 na dare inda ta cigaba da ci har zuwa lokacin da masu kashe gobara suka karaso.

A yayin da ya ke tabbatar da faruwar al'amarin, kwamishinan 'yan sanda na jihar ta Borno, Mista Abdu Umar, ya bayyana cewa jami'ansu da sauran jami'an tsaro sun yi aiki tukuru domin kashe gobarar, inda ya bayyana cewa kimanin motocin kashe gobara biyar aka tura wurin domin kawo karshen al'amarin.

An dai bayyana cewa an ga daruruwan 'yan kasuwa wadanda abin ya shafa suna kokarin tseratar da kayayyakin su a yayin da wasu kuma suka sa ido kawai yayin da wutar ke cigaba da ta'azzara.

Ana dai sauraron jawabi na musamman daga gwamnatin jihar.

No comments

Powered by Blogger.