Header Ads

Gobara ta kara tashi a kasuwar Singa da ke Kano

Gobara a ranar Litinin ta kama wasu shaguna da kuma saman tsohon ginin Savannah Bank da ke kasuwar Singa a jihar Kano.

Alhaji Saminu Abdullahi, jami'in hulda da jama'a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ya tabbatar da afkuwar hakan a cikin wani jawabi da ya yi a ranar Litinin.

Kamar yadda ya bayyana, wutar ta fara ne da misalin karfe 2:18 na dare.

"An yi mana kiran neman taimako da misalin karfe 2:18 na dare daga Sa'idu Hamza cewa akwai gobara a wata kasuwa wadda ke karamar hukumar Fagge da ke jihar.

"Bayan samun wannan labari nan-da-nan muka tada mutanenmu masu kashe gobara da kuma motocin kashe gobara zuwa wajen da misalin karfe 2:22 na dare domin su kashe gobarar kada ta shafi sauran shaguna."

Abdullahi ya bayyana cewa shaguna da dama na wucin gadi duk sun kama da wuta. 

Ya bayyana cewa har yanzu hukumar ba ta tantance adadin yawan shagunan da gobarar ta shafa ba.

No comments

Powered by Blogger.