Header Ads

Ganduje ya sa dokar hana fita a Kano bayan rashin nasarar APC

Gwamnan Kano Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya sa dokar hana fita a jihar Kano a ranar Litinin bayan an bayyana dan takarar jam'iyyar adawa ta NNPP, Abba Yusuf, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a jihar a ranar Asabar.

Abba Yusuf ya yi nasara ne a kan mataimakan gwamnan jihar, Yusuf Gawuna, wanda ke takara a karkashin jam'iyyar APC.

Jam'iyyar ta NNPP har wa yau ta samu mafi yawan kujeru a zaben da aka gudanar na 'yan majalisar jiha, sai dai dokar hana fita ta biyo baya sakamakon zaman dar-dar da ya biyo baya yayin tattara sakamakon zaben na gwamna da 'yan majalisun jihar.

Kwamishinan watsa labaru da harkokin cikin gida na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, a cikin wani jawabi da ya gabatar a ranar Litinin, ya bayyana cewa an sa dokar hana fitan ne domin hana 'yan daba yin amfani da halin dar-dar da ake ciki su haifar da yamutsi.

Kwamishinan ya yi kira ga mutanen jihar da su kasance a cikin gudajensu domin kuwa gwamnatin jihar ba za ta kyale duk wani mutum ko kungiya da ke neman haifar da matsala ba.

No comments

Powered by Blogger.