Femi-Fani-Kayode ya roki Allah ya tsine wa Emifiele da wasu a babban bankin Nijeriya
Tsohon ministan jiragen sama a Nijeriya, Femi Fani-Kayode da gwamnan babban bankin Nijeriya, Godwin Emefiele
Tsohon ministan jiragen sama a Nijeriya, Femi Fani-Kayode, ya yi addu'ar Allah ya yi shari'a tare da tsinewa gwamnan babban bankin Nijeriya, Godwin Emefiele da wasu domin cutarwarsu ga 'yan Nijeriya.
Duk da cewa kotun koli ta yanke hukunci, amma babban bankin ya ki bin umarnin kotun, inda rashin kudi ke kara hauhawa kuma yunwa ke karuwa a cikin kasa.
A cikin wani sako da ya rubuta, Femi Fani-Kayode ya yi fatar Allah ya yi shari'a kuma tsinuwarsa ta tabbata a kan Emifiele da wasu domin kin bin umarnin na kotu.
Ya bayyana cewa Emifiele da wasu a babban bankin Nijeriya suna yin wasu dabi'u kamar sun fi karfin dokar kasar nan ne kuma kamar sun fi mahaliccinsu.
"Da kudin ku, mulkinku, dukiyar ku da kadarorinku na dan wani lokaci ne." Kamar yadda ya bayyana.
Post a Comment