Header Ads

Falasdinawa da ke cikin kurkukun Isra'ila sun fara wani babban yajin kin cin abinci

Wasu Falasdinawa a cikin kurkukun Isra'ila

Wasu gungun Falasdinawa da ke cikin kurkukun Isra'ila sun fara yajin kin cin abinci sakamakon irin tsare-tsare na kasar ta Isra'ila masu cutarwa.

A cikin wani jawabi a ranar Laraba, kungiyar Falasdinawa da ke cikin kurkuku (PPS) ta bayyana cewa sama da wadanda ke cikin kurkuku 2,000 ne za su shiga cikin yajin kin cin abincin wanda za a fara ranar Alhamis, daya ga watan Ramadan.

Babban bakin cikin 'yan kurkukun shine tsare-tsare da dama da aka fara aiwatarwa masu cutarwa bayan umarnin da ministan Isra'ila, Itamar Ben Gvir, ya bayar.

Wannan yajin kin cin abincin an shirya shi ne domin a jawo hankali ga hakkokin da wadanda ke cikin kurkuku Falasdinawa ke da shi. Ana hana 'yan kurkukun damar samun kulawa da lafiyarsu kuma sukan fuskanci horo.

Daruruwan Falasdinawa 'yan kurkuku ana tsare da su ne karkashin ikon mulki, inda Isra'ila za ta kulle su ba tare da an caje su ba har tsawon wata shida, kuma za a iya kara tsawon wannan lokaci sau da dama ba tare da iyaka ba. Kungiyoyin kare hakkin bil-adama sun soki irin wannan tsare mutane da Isra'ilan ke yi.

Akwai dai kimanin Falasdinawa 7,000 a cikin gidajen kurkuku na Isra'ila, kuma hukumomin gidajen kurkukun na Isra'ila su kan ajiye 'yan kurkukun a muhallin da ba ya da cikakkiyar kulawa ta tsafta.

A ranar Litinin, majalisar Isra'ila, Knesset, ta amince da cewa yahudawa 'yan kama wuri zauna su dawo wuraren da suka tashi daga cikinsu tun shekarar 2005 da ke yankin da aka mamaye na yamma da gabar kogin Jordan.

Wannan yunkuri kuma ya haifar da suka mai karfi daga kungiyar fafutikar Falasdinawa ta Hamas. Wani mai magana da yawun kungiya, Jihad Taba, ya ce wannan kudirin yunkurinsa shine yahudantar da yankunan falasdinawa, to amma zai kara karfin fafutika ne kawai a cikin matasan Falasdinawa.

Yanke hukuncin sake zaunar da mutanen a yankunan hudu ya zo ne kasa da sati daya bayan Isra'ilan ta yi alkawari ga hukumomin Falasdinawa cewa ba za ta cigaba da yin gine-gine be a cikin akalla watanni hudu.

No comments

Powered by Blogger.