Header Ads

DSS ta kama mutum biyu a Kano kan zargin tayar da rikici

Isma'ila Iliyasu Mangu da DSS ta kama

Rundunar tsaron farin kaya ta DSS ta cafke fitaccen jarumin barkwancin nan mabiyin siyasar NNPP Kwankwasiyya, Habu Tabule da kuma wani mai suna Isma'il Iliyasu Mangu.

DSS ta ce ana zargin mutanen biyu da yin kalaman tunzura jama'a da neman a ta da tarzoma a zaɓen Gwamna da za a yi ranar Asabar.

Sharu Abubakar Tabula

Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter hukumar ta DSS ta ce mutanen sun naÉ—i hoton bidiyo ne da suke bayanan tunzura jama’a a cikinsu, sannan suka riÆ™a wallafa shi a shafukan sada zumunta.

“Cikin waÉ—annan saÆ™onnin masu haÉ—ari, sun nuna jam’iyyar siyasar da suke goyon baya kuma suka yi kira ga magoya bayansu su kai wa abokan hamayyarsu hari duk inda suka gansu.

“WaÉ—anda ake zargin sun yi kira da a kai wa jami’an tsaro hari yayin zaÉ“en gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi da za a yi a ranar Asabar.

“Wata jam’iyyar siyasa a Kano na barazanar shirya zanga-zanga a sakamakon shirin kai hare-haren,” in ji hukumar ta DSS.

Sanarwar ta Æ™ara da cewa jam’iyyar siyasar ta shirya kutsawa ofisoshin wasu hukumomin tsaro a ranar 16 ga watan Maris a matsayin nuna goyon baya ga waÉ—anda ake zargin.

“Yayin da hukumar ke sanar da mutane kan wannan haramtaccen mataki, ta kuma yi kira ga jam’iyyar da ta dakatar da wannan lamari, ko kuma ta shirya yaba wa aya zaÆ™inta.

“DSS ba za ta zuba ido tana kallon mutane suna tunzura al’umma ba su tayar da hankali da rashin tsaro a jiha ba.”

Sanarwar DSS ta ce za ta haɗa hannu da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da an samar da cikakken tsaron da zai bayar da damar da gudanar da zaɓe mai inganci a jihar.

Baya ga Kano hukumar tsaron ta kama wasu mutane da ke irin wannan kiraye-kiraye a wasu jihohi a faɗin ƙasar.

Hukumar ta shawarci jam’iyyun siyasa a fadin Najeriya da su gargadi mabiyansu su zama masu bin doka da oda, domin tabbatar da dimokuraÉ—iyya ta samu wurin zama yadda ya kamata.

No comments

Powered by Blogger.