Header Ads

Buhari ba ya mutunta umarnin kotu Cewar Kotun koli


Shugaban Kasa Buhari 

Kotun kolin Nijeriya mai mambobi guda bakwai ta bayyana shugaban kasar Nijeriya a matsayin wanda ba ya mutunta umarnin kotu a ranar Juma'a a cikin wani hukunci da ta yanke sakamakon wata kara wadda gwamnonin wasu jihohi suka shigar domin kalubalantar abinda suka kira tsarin gwamnatin Nijeriya na "cire kudade daga matsayinsu".

Kotun ta bayyana shugaba Buhari da wanda ba ya bin umarnin kotu a yadda ya mu'amalanci tsarin canza kudaden na Nijeriya.

Kotun kolin ta Nijeriya mai mambobi bakwai, Alkali John Okoro ne ke jagorantar ta.

"Rashin bin umarnin kotu da shugban kasar ya yi a wannan mulki na damakaradiyya da ke da kundin tsarin mulki, alama ce ta faduwar kundin tsarin mulkin kuma tsarin damakaradiyyar a baki ne kawai, mulkin ya koma na mutum daya ko kama-karya." Kamar yadda Emmanuel Agim, wani mamba a kotun kolin, ya bayyana a yayin hukuncin nata.

Tsarin, wanda babban bankin Nijeriya (CBN) ya kirkiro a cikin watan Oktobar shekarar da ta gabata, ya hada ne da samar da sabbin kudade da aka sauya fasalinsu na N200, N500, da N1,000 da kuma janye tsofaffin takardun da ke nan a cikin karamin lokaci.

Daga farko sun ayyana 31 ga watan Janairu ne domin tsofaffin kudaden su rasa amfaninsu a matsayin kudi sai kuma aka kara lokacin zuwa 10 ga watan Fabrairu a yayin da ta bayyana a fili cewa babban bankin na Nijeriya ba zai iya samar da sabbin takardun kudin ba a ko'ina.

Tsarin wanda shugaban kasar Nijeriya ya amincewa da shi ya kuma bada umarnin sa ya haifar da karancin kudade. Wannan kuwa, sai ya haifar da yamutsi, kawo matsaloli ga harkokin kasuwanci da samar da wahalhalu ga miliyoyin 'yan Nijeriya wadda kasa ce da tattalin arzukin ta ya doga da takardun kudi.

Gwamnonin jihohi uku - Kaduna, Kogi da Zamfara - sun shigar da karar gwamnatin tarayya a kotun koli a kan al'amarin a ranar 3 ga watan Fabrairu, inda suke nema da a rushe tsarin.

A ranar 8 ga watan Fabrairu, kwana biyu kafin wa'adin na babban bankin Nijeriya ya cika a ranar 10 ga watan Fabrairu domin kawo karshen amfani da tsofaffin takardun N200, N500 da kuma N1,000, kotun kolin ta sanar da hukuncin wucin gadi domin tsayar da tabbatar wa'adin tsarin.

Kotun ta bayyana cewa tsofaffin takardun kudin da kuma sabbin kudin duka su cigaba da kasancewa da matsayinsu har sai ta yanke hukunci.

To saidai Buhari ya nuna rashin mutunta umarnin kotu, domin a cikin wani jawabi da ya yi a ranar 16 ga watan Fabrairu, ya bayyana N200 ce kawai ta ke a matsayin wadda za a cigaba da amfani da ita, ya kuma dage a kan cewa tsofaffin takardun N500 da N1,000 ba za su kasance a matsayinsu na kudi ba.

 "Wanda aka shigar kara bai mutunta hukuncin kotu ba, ba wanda zai musanta hakan. Jawabin shugaban kasar na ranar 16 ga watan Fabrairu wanda ya ke a nan yanzu haka daga shafi na 27 zuwa 31 na nuni da wannan rashin mutuntawa." Agim ya bayyana.

Inda ya kara da cewa,"Domin nuna rashin mutunta umarnin kotun, ya bayyana cewa N200 ce kawai za a cigaba da yin amfani da ita."

"To sai dai kuma abin mamaki, umarni da ya bayar din ma ba a ga alamun ana amfani da shi ba. Na yarda da abinda mai kara na 9 ya fada, cewa wanda ake kara bai kamata a saurare shi a wannan kotu ba domin ya ki girmama wannan kotu da kuma matsayin doka wanda daga nan ne shugaban kasa ya samu ikonsa da kuma ikon gwamnatin tarayya."

Mr. Agim ya bayyana cewa rashin girmama umarnin kotu da Buhari ke yi ya mayar da gwamnatin ta damakaradiyya ba cikakkiya ba.

"Tsari na bin doka wanda a kan shi ne mulkin damakaradiyya ya doru ya zama ba cikakke ba in har shugaban kasa ko kuma wani mai mulki ya ki bin umarnin da kotu ta bayar." Kamar yadda alkalin kotun ya bayyana.

Kotun dai ta yi watsi da tsarin ne a ranar Juma'a domin shugaban kasar ya zartar da shi ne ba tare da ya tattauna ba kamar yadda ake tsammani a mulki irin na damakaradiyya.

Kotun ta kara wa'adin tsofaffin kudaden har zuwa 31 ga watan Disambar wannan shekara kuma ta bayar da umarnin cewa tsofaffin takardun kudi su kasance tare da sabbin kudaden har zuwa cikar wannan wa'adi.

Buhari, wanda ya taba yin mulkin soja tare da kasancewa wanda ba ya da shaida mai kyau dangane da kare hakkokin bil-adama a shekarun 1980s, ya yi kamfe a shekarar 2015 domin a zabe sa a matsayin shugaban kasa na farar hula tare da yin alkawarin kasancewa mai mulki irin na farar hula.

To amma tun bayan hawan sa karagar mulki, bai iya cika duka alkawuransa ba, domin kuwa gwamnatin sa kan zabi wace dokar kotu ce za ta yiwa biyayya a cikin tsawon shekaru bakwai da rabin shekara tun farawarta.

Sanarwar ta ranar Juma'a ta kasance ta farko wadda kotu ta yi a kansa cewa ba ya mutunta umarnin kotu.

No comments

Powered by Blogger.