Header Ads

Barayi sun sace kayan asibiti a garin da gwamnan jihar Ogun ya fito


Barayi sun afka cikin wani asibiti mai daukar gadaje 100 mai suna Mother and Child Hospital wanda aka bude watan da ya gabata a garin Iperu, karamar hukumar Ikenne, da ke jihar Ogun tare da sace kayayyaki na miliyoyin nairori. 

Asibitin dai mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ne ya bude shi, kuma a garin da ya ke na Iperi daga nan ne gwamnan jihar ta Ogun, Dapo Abiodun, ya fito.

Sai dai kungiyar tsaro ta jihar, Amotekun Corps, ta bayyana cewa ta kama mutane uku da ake zargin suna da hannu a cikin al'amarin, inda shugaban kungiyar David Akinremi, ya tabbatar da afkuwar al'amarin ga 'yan jaridu a Abeokuta a ranar Juma'a.

Mista Akinremi ya bayyana cewa barayin sun sace talabijin na Hisense masu inci 43 guda shida, talabijin din Bruhm masu inci 65 guda biyu, firiji guda uku na Bruhm, wani firiji na Midea guda daya da kuma dogayen fankoki wadanda ake yiwa caji guda uku, duka wadanda kudin su ya kama miliyan uku.

Ya kara da cewa an kama wani mutum mai suna Ogunjembola Kehinde wanda ya jagoranci sauran wadanda ake zargin su suka yi sata a asibitin.

Kwamandan kungiyar ya bayyana cewa an kama Ogunjembola ne bayan koken da wata mata Kehinde Banjoko ta shigar, inda ta bayyana cewa an shiga gidan ta an yi mata sata bayan tafiyar ta Legas.

Abubuwan da matar ta ce an sace mata sune tukunyar gas, janareto, fanka, katifa da kafet, duka kudadensu jumulla N500,000.

Bayan an tsananta bincike, babban wanda ake zargin ya amsa laifin sa, kamar yadda kwamandan ya bayyana, kuma an samu karbar duka kayan daga wani mutum mai suna Lawal Aliu. 

An dai kama mutanen da ake zargi akalla mutum uku, ana kuma cigaba da bincike domin samun sauran mutanen da wadanda ake zargin suka fada domin samun sauran kayayyakin da suka rage.

No comments

Powered by Blogger.